Jonathan  ya tsallake rijiya da baya,  muƙarrabansa biyu sun rasu a haɗarin mota

Jonathan  ya tsallake rijiya da baya,  muƙarrabansa biyu sun rasu a haɗarin mota

A jiya Laraba ne dai tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan ya yi haɗari, wanda ya kai ga rasa mukarrabansa na tsaro su biyu.

Har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin, amma kamar yadda Aminiya ta ruwaito, hadarin ya afku ne a lokacin da tsohon shugaban ke kan hanyarsa ta zuwa gidansa da ke Abuja daga filin jirgin sama.

Mai taimakawa Jonathan kan harkokin yada labarai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa.

Da yake tsokaci kan lamarin, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya ce, “Wannan labari ya girgiza mu. Muna godiya ga Allah da ya tseratar da rayuwar shugaban kasa @GEJonathan. Amma abin takaici ne yadda ya rasa mataimakansa biyu a hadarin mota.

“Ina ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma Shugaba #Jonathan. Allah ya jikan wadanda suka rasu ya huta lafiya," in ji Atiku.