A Yaushe Ne Rayuwar Mata A Karkara Za Ta Sauya?
Haka kuma idan an samu juna biyu, matan karkara awo ba dole ba ne a wurin mazajen su, ko da ya kasance matan na son tafiya awon, komai nisan asibitin. In haihuwa ta zo da barkwanci sai dai jike-jiken maganin gargajiya, in ba a yi nasara ba ne, dole za a dauko mai nakuda saman jaki ko amalanke zuwa asibitin da ba wata cikakkiyar kayan kulawa da ma’aikata, a hakan za ta kasance ko ta yi rayuwa ko ta mutu, ko ciwon yoyon fitsari ya same ta. In da daga baya miji ya kasa iya zama da ita da ciwon, sai ka ga an zo asibitin birni da ita, wannan ba karamar musiba ba ce. Wahalar da ke tattare da matan karkara ne ke sanya ka ga mace ‘yar kimanin shekara 20 sai ta koma kamar mai shekara 40, za ka ga mace da kyau amma ta koma mummuna, saboda bakar wahala da………………..
RAYUWAR MATA A KARKARA
“Mata in baku ba gida wajen Allah ku ash’shika-shiki, mata ku yi Aure kuma ku zan ka addini shi a rikon gida.”…………. MAWAKI MAIDAJI SABON BIRNI.
Mata su ne malamai na farko a cikin kowace al’umma su ke daukar ciki, su Haifa, su rena kuma su tarbiyantar, kuma a lokaci daya su ne ke kula da dawainiyar miji da ta ‘yan uwansa, duk wannan hobbasar da mata ke yi, a karkara bayi ne da ake amfani da su a jefar, watau dai mace ba mutum ba ce a wajensu.
A binciken da Managarciya ta aiwatar, ya nuna mafi yawan al’ummar Najeriya kashi saba’in (70%) daga cikin 100 suna zaune ne a karkara watau kauyukka, wanda idan an bi wannan kididdigar mata goma da ke rayuwa, bakwai daga cikinsu na zaune a karkara kenan. Mata mazauna karkara suna rayuwa ne ta bauta, hagu wahala, dama wahala, tsakkiya wahala.
Matan karkara ba su da lokacin hutu, tun duhun safiya sun tashi barci, wasu daga cikinsu za su fara da dibar ruwa daga gulabe ko Rijiya, ba a dogaro da matasan da ake da su a dibar ruwan ba don karancinsu ba, duk da lokaci-lokaci suna yawan tafiya birane (Ci rani).
Wasu daga cikinsu ne ke hawan rumbu (rehewa) dibar damen gero a sussuka, bayan nan su sarrafa shi su mayar da shi fura su kai gona a wurin manoma, a matsayin abincin rana watau (Lomi) wasunsu ma su kan koma da La’asar sakaliya akai wani abinci.
Dukkanin wannan jan aiki da suke yi, mai farawa tun a kiran sallar asuba na farin, har zuwa karfe biyar na yamma ba za su kare ba, wani lokaci har suna iya kai takwas na dare ko fiye da haka. Bayan haka, a lokacin da su ke son su yi wanka mafi yawan lokutta ruwan sun kare ga aikace-aikacen yinin.
Haka dai matan na karkara ke ta fama, in da abin ke kara ba ka tausayi shi ne, a lokacin azumin Ramadan ga yunwa ga kishi, amma ba wani aiki da ya canza karuwa ma yake yi, wasu matan ana shan ruwa (buda baki) sai daura abincin sahur, domin wasu mazan dole sai sabon tuwo da sabon damun fura suke iya ci ko sha a lokacin sahur.
Haka kuma idan an samu juna biyu, matan karkara awo ba dole ba ne a wurin mazajen su, ko da ya kasance matan na son tafiya awon, komai nisan asibitin. In haihuwa ta zo da barkwanci sai dai jike-jiken maganin gargajiya, in ba a yi nasara ba ne, dole za a dauko mai nakuda saman jaki ko amalanke zuwa asibitin da ba wata cikakkiyar kayan kulawa da ma’aikata, a hakan za ta kasance ko ta yi rayuwa ko ta mutu, ko ciwon yoyon fitsari ya same ta. In da daga baya miji ya kasa iya zama da ita da ciwon, sai ka ga an zo asibitin birni da ita, wannan ba karamar musiba ba ce.
Wahalar da ke tattare da matan karkara ne ke sanya ka ga mace ‘yar kimanin shekara 20 sai ta koma kamar mai shekara 40, za ka ga mace da kyau amma ta koma mummuna, saboda bakar wahala da rashin cin abinci mai gina jiki, wanda wannan ya na iya shafar abin da ke cikinta (juna biyu) in har tana da shi, in an yi nasara ta haifi cikin sai a rasa samun girman yaro ya kai dai-dai na karninsa na uwar da ke da hutu da samun cikakkiyar kulawa a birane.
Sannan wani abin takaici, za ka ga karkara an barta daga mata sai kananan yara, dukkanin mazan sun wuce kurmi wurin nema, wata hudu zuwa shida miji ba ya gida, sai sako kawai daga mijin, kuma aiken bai taka kara ya karya ba.
Wasu kauyuka da Managarciya ta shiga da suka hada da Aliyar Fulani da Aliyar Hausawa da ke cikin mazabar Sakkwai a karamar hukumar mulki ta Tangaza a jihar Sakkwato, garuruwan sun yi shekaru da dama da kafuwa, amma har yanzu ba injimin nika (markade) komai da hannu suke kowane irin aiki, babu makarantar zamani ko daya a kauyukkan.
Baka san lokacin da ci gaba zai same su ba, domin babu wani mai ilmi da za su iya fitarwa daga wannan karkarar duk da kowane lokaci ‘yan siyasa na shiga yakin neman zabe (domin neman kuri’un matan karkarar) wurin, amma babu ko dakin shan magani.
Kauyukkan kananan hukumomin Anka da Maradun da Maru da ke jihar Zamfara su ma hakan matan su ke rayuwa irin matan karkarar Sakkwato. Ka samu gida mai yawan iyali, matan aure uku da yara sha biyar, amma ba a dora tukunya a dafa abinci da rana, sai a ranar wata hidima ta biki, a gidan mai hali ko hakimi kenan, shi talaka ko abinci dare ba a rika yi gidansa, kullum ana yi ana tsambare, a dukkan wadannan karkara suna maraba da biki, saboda a lokacin ne kawai suke ci su koshi. Cin rana daya koshin wata, yanda ake kiran wannan koshin a wuraren.
Jihar Kebbi na da banbancin rayuwar matan karkara da takwarorinta amma ba sosai ba, kawai karin wahalar da matan suka fi na sauran shi ne noma, matan Kebbi musamman mutanen Zuru da Wasagu da Bena da Ribah da sauran wasu bangarori na jihar, za ka samu mata na zuwa gona kamar maza, kuma duk abin da namiji ke yi a harkar noma mace ba a dauke ma ta ko daya. Haka za ka samu suna yi ba dare ba rana, wahalar ciyar da gida ba na namiji kadai ba ne, har da matan, amma kuma reno mazan sun ki yarda su ri}a. Za ka samu mace da goyo tana duke da fartanya, a lokacin da uban yake zaune gindin bishiya, yana hira ko barcin sa.
A wajen dafuwar abinci ma, maza sun yarda matan ne kadai ke yin wahalar nemo itace da kunna wuta da gyara abinci, anan mazan ci ne kawai aikinsu. A haka wadannan wurare yaushe ne mace za ta zama mutum?
Wannan yanayin rayuwa mai kama da rayuwar bauta da kunci da rashin tabbas yana da kyau gwamnati ta yi kokarin kai abubuwan more rayuwa cikin karkara domin samun rayuwarsu ta inganta.
Haka kuma yana da kyau kungiyoyi masu zaman kansu su rika kai dauki ga irin wadannan wurare domin samar musu tallafi, su rayu kamar kowa rayuwa mai inganci.
Daga Ummu Mika’ilu