Kocin Super Eagles, Peseiro ya ajiye aiki

Kocin Super Eagles, Peseiro ya ajiye aiki

Kocin tawogar ƙwallon ƙafar Nijeriya, Super Eagles, Jose Peseiro, ya tabbatar da ajiye aiki a matsayin koci bayan kwantiraginsa ta kare a hukumance a jiya Alhamis.

Peseiro, wanda ya jagoranci Eagles zuwa matsayi na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023, a yau Juma'a, ya ce ya kammala aikin sa na horas da tawogar ƙasar.

“A jiya mun kammala kwantiragin mu da NFF. Abin alfahari ne da girmamawa ga kocin Super Eagles. Ya kasance watanni 22 na sadaukarwa, tausayawa, da kuma girmamawa. Mun samu gamsuwa a aikin

“Muna son mika godiyarmu ga Sir Amaju Pinnick, Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kasa Ibrahim Gusau, Babban Sakatare Mohammed Sanusi, Sakatare Dayo Enebi, da Hukumar NFF, da daukacin Ma’aikatan NFF, musamman ma daukacin ’yan wasan, wadanda na ji dadin aiki da su sosai.