EFCC ta gurfanar da surukin Tambuwal  a gaban kotu kan zargin sama da faɗi da miliyan 419

EFCC ta gurfanar da surukin Tambuwal  a gaban kotu kan zargin sama da faɗi da miliyan 419
EFCC ta gurfanar da surukin Tambuwal  a gaban kotu kan zargin sama da faɗi da miliyan 419
 
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa waton EFCC ta gabatar da Sanata Umaru Tafida Argungu gaban Alƙali Mohammed Mohammed a babbar kotun jihar Sakkwato kan tuhuma ɗaya waton zarginsa da yin sama da faɗi da dukiyar jama'a ₦419,744,612.30.
A cewar bayanin da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar ya ce tsohon Sanatan da ya waƙilci Kebbi ta Arewa a majalisa ta 6 ana zarginsa da ya yi kwana da wani kaso  na hannun jari da gwamnatin Sakkwato ta saya da zai kai kashi 40 a Kamfanin Hijira wanda yake mallakar kamfanin Saƙa na Hijirah ne.
Ya ce gwamnatin Sakkwato ta ƙulla yarjejeniya da tsohon Sanatan za ta saye kashi 40 na hannun jarin kamfaninsa don samar da aikin yi ga matasa da bunƙasa tattalin arziki a jihar.
A cewar bayanin da aka fitar Mista Uwajeren ya ce bincike ya bayyana yadda aka yi ta fitar da kuɗin ana kuma turawa ga wasu asusun ɗaiɗaikun mutane wanda hakan bai da alaƙa da abin da aka baiwa kamfanin kuɗin. Da masu bincike suka ziyarci kamfanin sun samu an fita batun kamfanin yana cikin halin ni 'ya su.
Mai gabatar da ƙara ya karantawa Sanata wanda shi ne shugaban kamfanin na Hijira daga 2016 zuwa 2017 irin laifin da ake tuhumarsa na aikata rashin gaskiya da sama da faɗi da kuɗin jihar Sakkwato in da nan kamfanin yake da zama kan haka babbar kotun jiha ke da hurumin sauraren ƙarar laifin da ake tuhumarsa da ya saɓawa kundin dokar jiha a sashe na 311.
Surukin na Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal bai karɓa laifin da ake tuhumarsa ba.
Lauyan masu ƙara S. H Sa'ad ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari'ar kan haka lauyan wanda ake ƙara Ibrahim Abdullahi ya nemi beli ga kotu.
Alƙali Mohammed ya aminta da ba da belin wanda ake tuhuma kan miliyan 50 da mutum biyu da za su tsaya masa dake zaune in da kotu take da hurumi, ya kuma ba da fasfo nasa.
Alƙali ya sanya 18 ga watan Maris 2021 don fara shari'ar.