'Yar wasan Hausa ta nemi jama'a su yafe mata bayan da ake raɗe-raɗen ba ta da lafiya 

'Yar wasan Hausa ta nemi jama'a su yafe mata bayan da ake raɗe-raɗen ba ta da lafiya 

Maryam Yahaya Ta Nemi Al'umma Su Yafe Mata A Daidai Lokacin Da Wasu Ke Zargin Cewa Tana Kwance Ne Rai A Hannun Allah

Jaruma a masana'antar Finafinan Hausa ta Kannywood, Maryam Yahaya ta nemi dukkan mutanen da ta yi wa ba daidai ba su taimaka su yafe mata a daidai lokacin da wasu ke zargin cewa tana kwance ne a gadon asibiti ba lafiya.

Maryam, ta nemi yafiyar ne a shafinta na Instagram kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito inda ta ce, "Assalamu Alaikum, dan Allah duk wanda na yi wa laifi ya yafe min. Na gode". 

Hakan ne ya sa wasu ke ganin Jarumar tana cikin matsananciyar rashin lafiya ne shi isa ta bayyana hakan, amma dai zuwa yanzu babu cikakken rahoto kan haƙiƙanin halin da take ciki.