Zargin Kama matashiya a Sakkwato: Yadda lamarin yake--- ‘Yan sanda
Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta fitar da wani bayani wanda jami’in hulda da jama’a na jiha ASP Ahmad Rufa’i ya rabawa manema labarai a jiha ya ce hankalin rundunar ‘yan sandan ya karkato kan wata karya da shaci fadi da ake yadawa a kafofin sada zumunta da sauran kafafen yada labarai wai rundunar ‘yan sandan Sakkwato a asirce ta kama wata mata saboda ta soki Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu.
“Wannan karya ne kuma shaci fadi ne, yadda lamarin yake, a ranar 3 ga watan Nuwamban nan, Marafa Yakubu hakimin Sabon Birnin Daji a karamar hukumar Wurno ya kawo bayani wurin 'yan sanda cewa wata mata da ake kira Hamdiyya Sidi wadda ita 'yar kauyen Munki ce duk a karamar hukumar, ta zo kauyensa ta yaudare shi in da ta gaya masa ita tana cikin kungiyoyin da ke tallafawa al'umma don haka ta zo nan don ta taimaki mata da matasa, tana son ta yi masu jawabi sannan a tallafawa marasa karfi."
Ya ce a lokacin da take yi masu jawabi ne ta yi kalaman fusata matan ga gwamnati hakan ya haifar da rudu a cikin jama'a, sai jami'an tsaron yankin suka kama ta suka mika ta hannun 'yan sanda.
Jami'in hulda da jama'a ya ce wa wadda ake tuhumar a lokacin da take wurinsu ta karbi laifinta na haifar da rudu a cikin al'umma daga nan suka kaita kotu a cikin awa 24.
Ya ce dokar kasa ta daura masu alhakin bincikar kanana da manyan laifukka, abin da ya shafi Hamdiyya ba zai fita daban ba.
Ya yi kira ga mutane su daina yada karya a cikin al'umma domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.
managarciya