Gwamnan Kebbi Ya Rabawa Kwamishinoninsa Motocin Alfarma 27 Da Babura Ga Yan Sintiri 700
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Gwamnan jihar kebbi Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya kaddamar da wani shiri na rabawa Kwamishinonin jahar motocin alfarma 27 domin inganta ayyukan jihar.
A kokarin yaki da 'yan bindiga da suka addabi jihar kebbi gwamanatin jihar ta kaddamar da rabon babura ga jami'an tsaron 'yan banga sama da 700 ta yadda za ta yi yaki batagari domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
Gwamnatin Kebbi tace ta samar da wadannan babura ne ga yan sintirin ne da za su gudanar da aiki da jami'an tsaro abinda ta ce zai taimaka a kokarinsu na kawar da yan ta'adda da suka addabi jihar kebbi.
managarciya