Abin da ya bambanta Mariya Tambuwal da sauran matan Gwamnonin Nijeriya

 Abin da ya bambanta Mariya Tambuwal da sauran matan Gwamnonin Nijeriya

Mariya Tambuwal  haifaffiyar  garin Sanyina ce a ranar 27 ga Afirilun 1978, cikin karamar hukumar mulkin Tambuwal, ta yi karatun Firamare dinta a Firamaren Sanyinna,  bayan ta  kammala ne ta wuce makarantar mata ta Illela (Unity Girls Secondary School Illela) tana gama sikandare, ba ta tsaya ba ta wuce kwalejin kimiyya wato umaru ali shinkafi polytechnic ta yi difiloma kan fannin shari’a a 1993-1995(diploma in law). 

A  lokacin da mai gidanta ya samu zama kakakin majalisar dokoki ta kasa (2011-2015) ta kara daure damara da sadaukarwata a gare shi domin cimma burinsa na rayuwa, a  kokarin  macce ga mijinta don samar da iyali da al’umma tagari. Ta kirkiro shiraruwan  cigaban mata da matasa da tallafin ilmi da wayarwa  mata  kai kan sha'anin kiyon lafiya musamman mata masu renon ciki da  kananan yara.

Allah mai iko a lokacin da jagorancin mutanen jihar Sakkwato ya hau kansu, uwar gidan gwamna ta rungumi aiki babu kama hannun yaro ta fito da abubuwan cigaban yara da ba su nishadi, takan je makarantu ta gani da idonta halin da ake ciki. Bata tsaya anan ba ta kutsa kanta ga samar da hanyoyin wayar da kai,  domin samun zaman lafiya tsakanin kabilu daban-daban, da wannan tunanin nata ne, ta sanya hikima cikinsa in da ta ke shirya buda bakin azumin Ramadan, da shirya muhawarorin ilmin dalibai 'yan makaranta, ga kuma tsaya wa  a ji koken jama'a a ta hanyar tattaunawa da jagororinsu da su kansu talakawa a cikin sakin fuska da annashhuwa, kusan ba ta da wani lokaci na hutawa ko shakatawa ko yawon buda ido wanda ya wuce ziyarar marar sa lafiya, gajiyayyu da kuma marar sa galihu,mafi yawancin lokutta a duk sadda take cikin nishadi takan ziyarci Marayun Allah taci abinci tare da su domin ta faranta musu rai susan cewa suna da gata a cikin al’umma, wannan dalilin ne yassa ake kiran ta da suna Uwar Marayu.

Uwar Marayu dai burinta Matasa, Mata da kuma Marayu a jihar Sakkwato su samu walwala da farinciki a zamanin mulkinsu, halayyar da ta banbanta ta da dukkan matan gwamnonin kasar nan ta Nijeriya.

Hajiya Mariya ta kirkiri wata GIDAUNIYAR  sa-kai,  don kara inganta taimakon mata da kananan yara da marasa galihu a cikin alumma da hukuma ta aminta da ita mai suna MARIYA TAMBUWAL DEVELOPMENT INITIATIVE (MTDI) ta yi haka ne don taimakon ya tsayu da kafafunsa ya iya shiga a kowane lungu da sakon Sakkwato,

 

Kalubalenta na rayuwa

Kalubalenta bai fi rashin fahimtar da ke ga mutane na bambancin gidauniya da gwamnati ba duk abinda gidauniya ta yi sai a dauka na gwamnati ne; ba su fahimci cewar gidauniya tana marawa ayyukan gwamnati ne ba, domin kawo cigaba mai amfani.amma alhamdulillahi an fara fahimta allah ya kara yi muna jagora.

Darasin da ta koya na rayuwa.

"To kasan rayuwa mai juyawa ce koyaushe, ko ta zo da abu mai kyau ko akasinsa, amma dai kowane mutum yana   bukatar ya samu rayuwa mai kyau a kullum, hakan ne zai jagorance shi a samun nasara, darasin rayuwa ya kara sanya ni, rike gaskiyar dana taso da ita a cikin kowane lamari, don na tabbatar duk wanda ya rike gaskiya ba zai fada halin danasani ko kaico ba.

"Burin da nake da shi bai wuce na zama mai nutsuwa da hankali, da yiwa yarana tarbiya kamar yadda aka yimin;kuma ina da kudurin ganin mata yan uwana sun tsayu da kansu yara kanana sun daina barace barace.ilimin yara mata ya inganta a karkashin gidauniyata da yardarm allah. " a cewar Mariya Tambuwal.  

Da ta juya kan rawar da mata kan iya takawa a cikin al’umma ta ce  'A lafiyayyen hankali mata da maza ba daya ba ne, amma mata suna da rawar da za su iya takawa ga al’umma, don su ne kashin baya al’umma masu iya magana ma, sun ce karantar da mace karantar da al’umma ne.' in ji uwar gidan gwamna.

Taimakonta ga marasa galihu a jihar Sakkwato

Taimakawa mata masu cutar yoyon fitsari a asibitin Maryam Abacha, lokaci-lokaci domin ganin masu cutar sun samu gudunmuwar da ta dace su san su ma mutane ne kamar kowa,da kuma shirya tarurruka daga lokaci zuwa lokaci dmin wayar da kan matasa akan rashin amfanin shaye shaye wanda hakan yayi  sanadiyar bude center ta warkar da masu shaye shaye a asibitin specialist wanda ta yi tare da hadin kan matan gwamnonin arewa bada dadewa ba;tana kuma bada tallafi ga yara mata a kai kai da kungiyoyin addinin musulunci domin suci gaba da fadakarwa;tana kuma ayyuka da kungiyoyin turawa domin taimkawa ta haujin lafiya kamar su  UNFA,plan ;USAID  da sauransu.  

Daga karshe tana kiraga matasa da su daina dabiar area boys su je makarnta su yi karatu domin a dama da su, kuma a yi alfahari da su.