Hana Sana'ar Acaɓa Gwamnati Za Ta Rasa Kuɗin Shiga Mai Yawa, Ta'addanci Zai Ƙaru---- Hajiya Hauwa Inuwa
Daga Habu Rabeel, Gombe.
Hajiya Hauwa Muhammad Inuwa, tsohuwar yar Takarar kujerar Sanatan Gombe ta arewa a jam'iyyar Accord tace tana mai kira ga gwamnati da ta janye kudurin ta na hana sana'ar Achaba a Najeriya domin kar a jefa mutane cikin kuncin rayuwa
Hajiya Hauwa Inuwa, ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a Gombe inda tace masu sana'oi daban-daban guda 7 ne suke cin abinci a dalilin Babura akwai masu Faci, masu sayar da bakin mai da makanikai da masu wanki da sauran idan aka hana ya za'ayi da su.
Tace idan gudun ta'addanci ne an san inda yan ta'addan suke a daji an kuma san yadda za'ayi a kama su ba'a nemesu an kama su ba sai masu neman halak ake kokarin hanawa menene ranar yin hakan so ake a taru a koma yan ta'adda baki daya.
Hauwa, ta kuma ce gwamnati ta janye wannan aniya na ta sannan kuma ta inganta wutar lantarki dan a gina masana'antu da kamfanoni da zai kara rage zaman banza.
A cewar ta idan aka ci gaba da kure talaka har ya kai bango hakan ne ke sa ya shiga ayyukan ta'addanci dan nemawa kan sa mafita wanda da haka ne masu garkuwa da mutane yan fashin daji suka samu sana'a har suka yi karfi.
A bangare daya tayi kira da su matasan da cewa suma kar su dogara a sana'a daya a raba hannu a samu wata sana'a a hada dan a rufawa juna asiri saboda koda an hana achaba mutum ba zai shiga wani hali ba.
Daga nan tace hatta ita gwamnati kan ta za ta yi asara domin masu sana'ar suna biyan ta haraji na kudi mai yawa wanda hana su din zai rage mata hanyar shigar kudi.
managarciya