Kotu ta bada belin hadimin Tambuwal da ya soki gwamnan Sokoto
Wata kotun Majistiri da ke jihar Sokoto a yau Laraba ta bada belin Shafi'u Umar, hadimin tsohon Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, kan Naira Miliyan 1.
Shafi'u Umar mai shekaru 37, ana zarginsa da yada karya kan Gwamna Ahmad Aliyu da matarsa a shafin sada zumunta na zamani.
Haka kuma ana tuhumar sa da bata suna.
A ranar 26 ga watan Agusta ne aka fara shari'ar, inda dan sanda dake gabatar da kara, Insp Abdulrahman Mansur, ya ce laifin ya saba da dokar Panel Code.
Acewar takardar rahotan farko, wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuli.
Takardar tuhuma ta ce wanda ake karar, ya yada bidiyon matar gwamnan, Fatima Aliyu tana "Lika" kudi a yayin bikin tunawa da ranar haihuwar ta a yayin da ake fama da matsin tattalin arziki a jihar.
Haka kuma an zargi Shafi'u Umar da wallafa takardun makaranta dake nuna Gwamna Aliyu ya fadi jarrabawar Turanci da kuma gazawar sa wajen iya harshen na turanci..
Wanda ake zargi ya musanta aikata laifin inda aka tura shi gidan Kuruku