Tambuwal Ya Naɗa Kwamishinoni Biyu  A Gwamnatinsa

Tambuwal Ya Naɗa Kwamishinoni Biyu  A Gwamnatinsa
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya aikewa majalisar dokokin jiha sunayen mutum biyu da yake son  a amince da su zaman kwamishinoni a gwamnatinsa.
Shugaban majalisar dokokin jiha Aminu Muhammad Achida ya ba da damar karanta takardar a gaban majalisa wadda gwamnati ta aiko.
 Mataimakin kilak a majalisar dokoki  Alh. Bello Ahmad Tambuwal ya karanta takardar da ke ƙunshe da sunayen biyu ALH. AKIBU DALHATU da ALH. DAHIRU YUSUF YABO. 
Majalisar ta amince mutanen za su bayyana gabanta a ranar Alhamis da ƙarfe 10 na safe.