Tsige Mataimakin gwamnan Zamfara a yi Hatara dai------ Gwamna Tambuwal

Tsige Mataimakin gwamnan Zamfara a yi Hatara dai------ Gwamna Tambuwal

 
Daga Hussaini Ibrahim.
 
Gwamnan Jihar Sokoto ,Aminu Waziri Tambuwal Kuma Dan takarar Shugaban Kasa a Jamiyyar PDP yayi kira ga 'yan majalisun Jihar Zamfara da suyi hatara da mutunta Shari'a a matsayin su na masu yin doka wajan tsige Mataimakin gwamnan Zamfara,Barista Mahadi Ali Gusau.</ div>
 
Tanbuwal ya bayyana haka ne a Gusau lokacin ziyarasa ta neman alfarma 'Yan Jamiyyar PDP da su mara masa baya wajan kudirinsa na fitowa takarar shugaban qasa a zaben mai zuwa .
 
Gwamna Tambuwal ya kara da cewa, matsalar Jihar Zamfara bata siyasa bace matsala ce ta magance matsalar tsaro da ta'addan Jihar da yankunan mu dan haka bai kamata ba, wasu su rudi 'yan majalisun wajan ganin sun kawo rudanin siyasa a cikin jihar.inji gwamna Tanbuwal.
 
" Mataimakin gwamnan Zamfara yana koto akan batun sa da su 'yan majalisar amma suna nema suyi riga Malam Masallaci akan haka ne Tanbuwal yayi kira da su mutunta Shari'a karda subi san rai na wasu .a cikin wannan lamarin.
 
Da koma kan takarar sa kuwa gwamna Tanbuwal ya bayyana cewa,suna neman goyan bayanan 'yan Jamiyyar PDP da su sake mara masa baya karo na biyu dan ya zamo dan takarar shugaban kasa a zaben na shekara ta 2023,dan Jamiyyar APC ta gaza ta kuwane  waje dan haka a shekara ta 2018,muka fice daga cikin ta muka dawo Jamiyyar PDP.inji gwamna Matawale.