Kina fama da ciwon bayan bayan tiyatar ciro jariri?
Uwaye da aka yi wa tiyatar ciro jariri, wato Caesarian Section" a turance, suna iya fuskantar ciwon baya bayan tiyatar.
Kafin tiyatar ana yin allurar anasiziya domin ɗauke ciwo yayin tiyatar.
Allurar anasiziya, sauye-sauyen sinadaran haihuwa, yankan tsokokin ciki da ɗauka ko goyon jariri ba daidai ba dukka na daga cikin dalilan da ke haɗuwa su janyo ciwon baya bayan tiyatar.
Hanyoyin magance ciwon bayan sun haɗa da: samun isasshen hutu, shan magunguna rage ciwo, ɗauka ko goyon jariri ta hanyar da ta dace da kuma ganin likitan fisiyo.
Saboda da haka, idan kina shan magungunan ciwon baya kuma ciwon yana ɗaukewa sannan ya dawo, to akwai buƙatar ganin likitan fisiyo domin magance ciwon bayan ba tare da dogaro da shan magunguna kullum ba.
managarciya