Buhari Ya Taya Sabon Gwamnan Anambra Murnar Lashe Zaɓe
Shugaba Buhari ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bisa nasarar kammala zaben da aka yi cikin nasara duk da tsaikon da aka fuskanta da farko. Haka zalika Shugaba Buhari ya umurci Mista Charles Soludo, wanda mamba ne a kwamitin shugaban kasa kan harkokin tattalin arziki, da ya tara masu ruwa da tsaki domin tunkarar manyan kalubalen da ke addabar jihar da kuma yankin kudu maso gabas.
Buhari Ya Taya Sabon Gwamnan Anambra Murnar Lashe Zaɓe.
Daga Comr Nura Siniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Farfesa Charles Chukwuma Soludo, dan takarar jam’iyyar APGA murnar lashe zaben gwamnan jihar Anambra.
Shugaba Buhari ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bisa nasarar kammala zaben da aka yi cikin nasara duk da tsaikon da aka fuskanta da farko.
Haka zalika Shugaba Buhari ya umurci Mista Charles Soludo, wanda mamba ne a kwamitin shugaban kasa kan harkokin tattalin arziki, da ya tara masu ruwa da tsaki domin tunkarar manyan kalubalen da ke addabar jihar da kuma yankin kudu maso gabas.
Shugaba Buhari ya ce zai yi aiki tare da gwamna mai jiran gado Charle Soludo, don samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban jihar Anambra da kasa baki daya, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar ya fada Mista Femi Adesina a shufuka shi na sada zumunta.
managarciya