Mata Suna Iya Jagoranci Nagari A Cikin Al'umma----Hajiya Hajara Aliyu Sanda
Yanzu dai ina da burin na zama ‘yar majalisar dokokin jiha mai wakiltar Sakkwato ta Arewa ta biyu, ina cikin gwagwarmaya kuma ina samun goyon baya domin ina son kawo cigaba wanda ba a taba kawowa ba, an yi wakilai da dama a gefenmu ba su yi abin da yakamata ba, in Allah ya bani damar sai mun gwadawa duniya mata suna iyawa ba sai maza ba, ina fatan Allah ya cikamin burina da samun rinjaye in ga mata sun samu wakilci a majalisa akwai kwamitin mata amma maza ke jagorantarsa wanda hakan bai dace ba, mata suke zabe amma an barsu baya yakamata su samu in da suke dafawa da ba su dama, suma su kwashi romon dimukuradiyya.
Daga Muhammad Nasir.
Hajiya Hajara Aliyu sanannar ‘yar siyasa ce da ta shahara wurin aiyukkan taimakon al’umma ta hanyar gidauniyarta da ake taimakawa matasa maza da mata domin ganin sun dogara da kansu da kawar da jahilci kansu, ta kudiri tsayawa takarar ‘yar majalisar jiha a jam’iyar APC sai dai an ci karfinta ta janye, a yanzu kuwa tana cikin kwamitocin yakin neman zabe a jiha da kasa baki daya, ta tattauna da manema labarai kan rayuwarta.
Tarihi a takaice
Sunana Hajara Aliyu Sanda an haifeni a garin Sakkwato, ina zaune a unguwar Rinin tawaye cikin karamar hukumar Sakkwato ta Arewa, na yi furamare da Sikandare da bautar kasa duka a Sakkwato, na yi karance-karance da dama bayan kammala jami’a, a takaice kenan.
Nasarorin Rayuwa
Sai godiyar Allah, babbar nasarar dana samu bai fi damar dana samu ta yin karatun ba, ganin yanda yake cike da kalubale tun daga matakin furamare saboda na tashi gida wanda ba’a karatun boko a gefen mahaifina, bayan na yi aure da goyo na nake tafiya makaranta domin ina son karatun ni nake daukar karatun har burina ya cika na kammala digiri, na kuma samu nasara in da na samu dama na taimaki al’ummata wurin samar da jari ga mata, yaran da ba su zuwa makaranta na dauki nauyinsu, sanadin alherin dana yi; ya sa mutane ke ganin yakamata na wakilce su a cikin shugabancin siyasa.
A matsayinki na mace wadan ne kalubale ne kika fuskanta kafin sunanki ya shahara a Sakkwato
Kalubale an fuskance su, musamman gefen karatuna domin gidanmu babban gida ne da muke da yawa a wurin mahaifinmu mun kai mu 58 masu rayuwa, gashi ana iya yi wa mace aure daga shekara 10, ga shi na kudurta cewa zan kafa tarihi a gidan na yi abin da ba a saba yi ba, hakan ba karamin kalubale na fuskanta ba sosai, da yake zuciyata nada jajircewa da nacewa, na yi sana’o’i kala-kala har nakai ga burina ya cika sai godiyar Allah.
Burinki na rayuwa ya cika kenan
Yanzu dai ina da burin na zama ‘yar majalisar dokokin jiha mai wakiltar Sakkwato ta Arewa ta biyu, ina cikin gwagwarmaya kuma ina samun goyon baya domin ina son kawo cigaba wanda ba a taba kawowa ba, an yi wakilai da dama a gefenmu ba su yi abin da yakamata ba, in Allah ya bani damar sai mun gwadawa duniya mata suna iyawa ba sai maza ba, ina fatan Allah ya cikamin burina da samun rinjaye in ga mata sun samu wakilci a majalisa akwai kwamitin mata amma maza ke jagorantarsa wanda hakan bai dace ba, mata suke zabe amma an barsu baya yakamata su samu in da suke dafawa da ba su dama, suma su kwashi romon dimukuradiyya.
Bayan baki nan mi kike son a tunaki da shi
Ina son na kafa tarihi a Sakkwato wanda har jikokina da dama ba za su manta da aiyukkan alherin dana shimfida ba, kamar irin Sardauna da Nana Asma’u Danfodiyo da sauran mata da suka kafa tarihi, ina son zama cikin jajirtattun mata da ake tunawa da su domin sun yin abin kirki shi ne fatana.
Akwai macen da kike koyi da ita cikin wadan da suka gabata
Akwai jajirtattun mata da yawa dana ke koyi da su don na zama kamar su, sai dai akwai wata ‘yar majalisa mace a yanzu wadda ba Bahausa ba ce da Hajiya Asabe da Hajiya Halima Hassan mace ta farko da ta fara zama ‘yar majalisa wakillan Nijeriya a yankin Sakkwato Kebbi da Zamfara lamurransu sun karamin kwarin guiwar nima naji zan iya, a lokacin da na fara nuna sha’awar shiga siyasa da yawan ‘yan uwana suka dauka wasa ce sai daga baya aka tabbar dagaske nake, ban da haufi domin na nemi addu’ar mahaifiya ta, tana tare dani domin na zama mai amfani ga al’umma.
Kina da Uban gida a harkokin Siyasa
A gaskiya ko da na fara harkar siyasa ban da wani wanda shi ne yacce naje na yi, ni ke da ra’ayina domin bana jin dadin abin da ke faruwa don haka nake son samun dama domin yin abin da ya dace, amma daga baya na hadu da masu bani shawara kan tafiyar da siyasa ta, hakan ya sa na samu magoya baya.
Mata na fuskantar Kalubale a wannan zamani mi kike ganin suke bukata don samar musu da mafita
Babban matsalolin da mata ke fuskanta musamman matan aure bai fi rashin samun wadataccen abinci da daukar takalihin rayuwarsu ba, ina ga in aka fito da hanyoyin samar da sana’o’in hannu ga mata don kyautata masu da ikon Allah za su samu abin da za su kula da kansu da iyalansu, a kuma fito tsarin daukar karatu ga yara kanana ana ba su tallafin karatu musamman ga masu hazaka matasa maza da mata za ka samu akwai masu basira suna son karatun amma ba wanda zai rika hannunsu a haka za a yi hasarar basirarsu ba ta amfani jama’a ba, in aka yi haka za a taimakwa al’umma daukar nauyin karatu abu ne mai wahala gwamnati kawai za ta taimaka a samu kai ga gaci, mata masu juna biyu akwai bukatar gwamnati ta dauke masu kudin magani a rika ba su shi kyauta. Matasa maza a rika shirya masu taron wayar da kai su guji harkar shaye-shaye wannan zai taimaka sosai.
Ana kallon Mata su ne matsalar kansu da kansu akwai shawara a wurinki
A in da muka fito mata ba sa goyon bayan junansu wanda hakan kowa ya sani kuma shi ya sa ake barinmu baya, amma yanzu an fara jingine lamarin kwalliya ta fara biyan sabulu mata mun fara hada kanmu domin ganin mun cigaba duk abin da babu hadin kai ba cigaba.