Tinubu zai sake Karbo bashin Tiriliyan  N1.77trn

Wannan bashin duk 'yan majalisar suka amince a karɓo shi ya ƙara nunawa talakawan Nijeriya ƙiyayyar su gare su, in har suna son talaka da ƙasa su hana ciwo wannan bashin.

Tinubu zai sake Karbo bashin Tiriliyan  N1.77trn

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta amince da sabon shirin rancen kasar waje na N1.767trn da Yake Shirin karbowa domin tallafawa kasafin kudin 2024.

Wannan bashin duk 'yan majalisar suka amince a karɓo shi ya ƙara nunawa talakawan Nijeriya ƙiyayyar su gare su, in har suna son talaka da ƙasa su hana ciwo wannan bashin.

Gwamnatin Tinubu tana yiwa tattalin arzikin Nijeriya kwasan karan mahaukaciya a lokaci guda majalisar ƙasa ta sa masa ido, a zo kan gaɓar da 'yan majalisar za su taka birki da wannan zaɓi ka dage da ake yi wa tattalin arziki.

Bashi don tallafawa kasafin kudi ba alheri ba ne ga tsarin tattalin arzikin kasa mafi dacewa ƙasa ta yi amfani da abin da take da shi maimakon ciwo bashin da zai ƙara karya darajar naira wanda hakan zai sa talaka ya kara shiga uƙuba da wahala.