Shahararren ɗan jaridar nan, kuma mamallakin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya zargi Mataimakin Shugaban Malissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da hannu cikin fitintinu masu nasaba da siyasa da ke faruwa a Jihar Kano.
A cewar Jaafar “Mutane da yawa su na tunanin Ganduje ne, Wallahi Barau ya fi hannu a wannan masifar. Su na shirya gidoga ne su faɗa wa shugaban ƙasa cewa mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati mai ci a Jihar Kano ba sa son ta idan ta yi taro aka gani da jama’a da yawa ya soke wannan zargi.
“Kusan duk wannan abubuwan da ake ƙullawa Wallahi da hannunsu. Ko ɗansanda za a kawo Kano sai wanda suke so wanda zai kare muradunsu.
“Irin wannan bai kamata ba. Ko takarar gwamna mutum zai yi, bai kamata ya kasaara al’umma ba. Irin wannan bai dace ba, ba kuma kishin jiha da al’umma ba ne,” in ji Jaafar Jaafarya.





