A Cikin Ramadan Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Sace Matafiya 

A Cikin Ramadan Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Sace Matafiya 

 

An sace matafiya da dama bayan yan bindiga sun bude wa motocci wuta a garin Iche, mai nisanta wasu yan kilomita daga garin Kagarko da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wani mazaunin unguwar, Shuaibu Yahaya, ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba jim kadan bayan an sha ruwa.
Shuaibu ya ce yan bindigan, dauke da bindigu kirar AK-47, sun harbi tayoyin motoccin don sace su, sannan suka rika zuwa mota zuwa mota suna tafiya da fasinjoji. 
"Karar harbin bindigan su ya janyo hankali na saboda gida na ba shi da nisa da wurin da abin ya faru. Yayin da wasu motocci sun fada tarkonsu, wasu da dama sun juya cikin gaggawa sun tsere." 
Basaraken gargajiya ya tabbatar da lamarin Madakin Janjala, Samaila Babangida, shima ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa: 
"A safiyar yau (jiya), an kira ni daga Kagarko cewa yan bindiga sun sace wasu fasinjoji a daren jiya, yan kilomita kadan daga garin Kagarko, amma ban san ainihin adadin wadanda aka sace ba." 
Mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna bai riga ya fitar da sanarwa kan afkuwar lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.