Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.

Maigirma hakimin Bosso, Alhaji Adamu Laka Bosso, yayi naɗin sarautu shida a fadarsa, waɗanda aka naɗan sun haɗa da Ambassada ( Dr) Nura Hashim a matsayin Tallafin Bosso ƙarami, sai Alhaji Yusuf Alkali a matsayin Dami-damin Bosso, Alhaji Adamu Zagi kuwa an naɗa shi Mabokan Bosso, sai Abubakar Ibrahim Aliyu wanda aka naɗa Dan-amen Bosso, yayin da aka naɗa Hon. Muhammad Sama'ila Ɗanbaba a matsayin Tambarin Bosso.
Tunda farko a bayanin hakimin ya bayyana cewar yayi wannan naɗe-naɗen ne ga ƴaƴan Bosso, saboda ƙwazon su da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban masarautar.
Amb. Dr. Nura Hashim ɗaya daga cikin waɗanda aka naɗan, ya godewa hakimin Bosso, bisa wannan karamcin da yayi mai na ba shi sarautar Tallafin Bosso.
Dr. Nura ya cigaba da cewar wannan karamcin abin alfahari ne gare shi, dan haka ya sha alwashin cigaba da tallafawa al'umma da lokacin shi, abin hannun shi da jikin shi dan ganin rayuwar al'ummar masarautar Bosso da Minna baki ɗaya.
Kamar yadda maigirma hakimi ya faɗi ya naɗa mu waɗannan muƙamai ne saboda irin gudunmawar da muke baiwa rayuwar al'umma, da yardar Allah, ba zan ja baya ba, kuma ba zan gajiya ba, dan haka ina jawo hankalin ƴan uwa da abokan arziki da su taimaka mana da shawarwarin da zasu cigaba kawo mana cigaba a yankin nan.
Da yake tofa albarkacin bakin shi, Alhaji Hashimu Bosso, mahaifin Ambasada Nura, yace yana mai farin cikin ganin tun ina raye Nura na cin ribar abinda ya shuka a rayuwa.
Dan haka ina jawo hankalin irin alheran da yake yi kar ya ja baya, saboda duk wata nasarar rayuwa tana tare da kyakkyawar niyya. Kamar yadda yazo ɗa mai biyaya haziƙi, ina roƙon Allah ya inganta zuri'arsa.
Malam Musa Isah ( Babawo) wani makusancin Dr. Nura, yace samun wannan matsayin da wannan bawan Allah yayi bai zo mana da mamaki ba, domin tun tasowarsa haziƙi ne mai tausayi. Kuma da yardar Allah za mu cigaba da ba shi shawarwari ta yadda zai cigaba da samun nasarar rayuwa.
Ƴan uwa da abokan arziki sun nuna farin cikin su kan wannan naɗin na tallafin Bosso, Farfesa Buhari Isah, gogaggen manazarcin yanayin rayuwar ɗan Adam kuma wanda ƙungiyarsa ta baiwa Nura Hashim matsayin jakada kuma Daktan a ɓangaren falsafa, yace duk irin muƙamin da za ka baiwa Nura Hashim ya cancance shi.
Masu riƙe da sarautun gargajiya da dama sun halarci naɗin, masu unguwanni da hakimai da dagatai daga fadar masarautar minna da gundumar Bosso na daga cikin makarta taron.