'Yan sanda sun kama Barawon da ya saci Babura 6  a Sakkwato

'Yan sanda sun kama Barawon da ya saci Babura 6  a Sakkwato
Rundunar 'yan sandan Sakkwato sun kama Kabiru Abubakar Aliyas mai shekaru 25 kan zargin ya sace Babur bayan da aka ajiye shi a Asibitin koyarwa ta Usman Danfodiyo kwana uku da suka gabata.
Wanda ake zargi ya yarda da laifinsa ya kuma kara da fadin wani mashin da ya sace a Asibitin Rahamat mallakar wani Naziru Muhammad, ya fadi wanda yake kaiwa Babur a unguwar Bello Way Kabiru Alhaji Yaro, da aka fadada bincike aka gano mashin shidda da ya sace.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar ASP Ahmad Rufa'i a bayanin da ya rabawa manema labarai ya ce wadanda ake zargi za a kai su kotu bayan an kammala bincike.