Matsalar Tsaro a Nijeriya ta Arewa Ina Gizo Ke Saka?

Matsalar Tsaro a Nijeriya ta Arewa Ina Gizo Ke Saka?

          A Nijeriya musammam ta Arewa, tarihi ya nuna cewa yanki ne mai zaman lahiya da wadatar arziki shiyassa a wancan lokaci, mutane suna unfanuwa da albarkatun da Allah ya wadata yankin da su. Suna da kasar  noma wadda kusan duk abinda an ka shukka ana samun albarka, ga wadatar dabbobin da Allah ya ba su. Lokaci yana tahiya, mutane suna zaune cikin aminci da kwnaciyar hankali. Kwatsam sai a ka waye gari da rahsin zaman lahiya da tashin hankali tsakanin mutane, babu wani dalili kwakkwara ana zuba da jinin mutane ana ta karya arzukin su.

          Mafiyawan masana suna danganta matsalar tsaro a wannan zamani da abubuwa  masu yawa. Amma asali lamarin ya samu ne sanadiyyar fadar manoma da makiyaya (Fulani). Wannan matsalar ko a tarihi daddaden abu ne, an san yana faruwa akai- akai a cikin garuruwa da kauyukka na wannan yanki. Idan ana iya tunawa tun zamanin Sarkin Musulmi Bello (1817-1837), tarihi ya nuna yayi ta sulhunta rikitta da fadace- fadacen Manoma da Fulani a garuruwa da dama a cikin kewayen Daular Usmaniyya.

          Matsalar  tsaron ta fara ne daga fadan Fulani da Hausawa (Manoma) kamar dai yadda bayani ya gabata. Ana kan haka sai abubuwa sabbi suka shigo lamari ya canza daga fadan  sai ya koma rashin tsaro gaba gadi a mafiyawancin Arewa ta yadda ake samun gugngun mutane da sun ka dauki makamai na zamani (bindigogi manya masu hadari) don kokarin huce haushin abinda manoma ka yi masu tare da dabbobin su, sai suka kama satar shanu. Wannan satar ta hada da kabilu da dama. Su kuma wadanda ake wa satar sai sun ka kudurce ramuwar gayya har wadda ta wuce wuri. Dama Bahaushe na cewa ‘ramau tafi farau ciyo’.

          Wannan lamarin na matsalar tsaro ta hada da satar shanu, mutane da ruguza dukiya ta samo asali ne dagga jahar Zamfara dake Arewa maso yamma. Kuma rahotanni sun tabbatar ta fara ne a shekara 2011 a garin Dansaadu dake karamar hukumar mulkin Maru inda wasu Hausawa (wadanda ake zargi sunyi ramuwar gayya na abinda ke tsakaninsu da Fulani), sun kama wani tsohon barawo (bafillace) wanda ya tuba su ka kunna masa wuta a bainar jama’a yakone kurmu mus. Haka sun ka yi ta yi a cikin wasu garuruwa kamar Dan Gulbi da sauran su, suna ta kashe tubabbin barayi. Su ko yan’uwan wadanda aka kashe sai su ka kama wasu daga cikin yan’uwan wadancan su ka ksahe, sai su kuma su ka kama sauran barayi da wadanda suka tuba da wadanda ke yin satar su ka kashe. Toh sai tubabbin barayin da wasu daga cikin yan’uwan su su ka tadda tuba kuma su ka shiga neman makamai suka fara farautar mutane suna kashewa su ka shiga kuma cikin satar shanu gadan gadan duk dai mafiyawan mutane suna alakanta barayin da cewa ba ‘yan Nijeriya ba ne. Da su ka ji dadin abinda su ka fara sai su ka cigaba su ka mai da lamarin sana’a in sun kama shanu su sayar sai su saye makamai su kara karfi, haka dai su ka cigaba har suka hada da satar mutane.

          Wannan lamari haka ya cigaba da tafiya tare da sakaci na gwamnatin jahar Zamafara da kuma gwamnatin Tarayya na rashin daukar kwakkwaran mataki don dakile abun tun yana karami har abin ya girma ya game jahar Zamfara. Sai lamarin yayi tahiya har ya shiga makwabtan jahohi daga Zamfara kamar: Katsina, Sokoto, Kaduna, Kabbi. Ya kuma kara ba gaba yakai Niger duk yakewaye sauran jahohin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakkiya haka nan da sauran jahohin Arewa. 

          Kada mu manta a gehe guda, akawai Boko Haram wadda ake kira ‘Jama’atul Ahalil Sunnah Liddawaatil wal Jihad’. Kungiya ce da Muhammad bn Yusuf na Maiduguri ya kirkira. Ayukkan ta mafiyawanci sun fi tasiri a Arewa maos gabas. Wannan kungiya ta fara kaddamar da ayukkan ta a shekarar 2009 kuma a wannan shekarar ce ta fara fada da gwamnatin Nijeriya. Kamar  yadda kowa ya sani wannan kungiya ta yi banna sosai fiye da tunani dan’adam, kuma tana kan yi. Mutane da dama suna bayyana cewa duk jama’a guda ne da masu satar shanu da mutane, illa dai sun raba ayukkan su ne don rudar da jami’an tsaro da sauran mutane,  suna amfani da masu garkuwa da mutane da masu satar shanu suna neman musu kudin shiga sai su ko suna kai hare-hare.

          Wannan lamarin na rashin tsaro ya addabe kusan kowa a wannan zamani musammam talakawa da basu da mai kare su in ba Allah ba. Lamarin ya jawo hasarar rayukka da ba wanda yasan adadin su ba in ba Allah ba, haka nan da dukiya mai yawa. Matsalar kuma ta kassara kasuwanci, neman ilimi shiyassa mafiyawan makarantunmu suna rufe a Arewa, kuma tafiya wasu garuruwa neman ilimi ya karanta saboda an kashe mutane ko a sace su don neman kudin fansa, an kuma kassara noma, manoma da yawa basu iya zuwa gona ko sun yi nomar ba a bari su girbe umfanin gonar. Shiyassa abinci ya yi karanci kuma ya nata kara tsada, mataloli da dama sun yawaita saboda rashin tsaro. Masana da dama suna ayyana abubuwa da yawa da su ka kawo matsalar tsaro a wannan yanki na Nijeriya kuma suke sa lamarin na ta kara zafafa yana ta kuma chanza sabon salo tayadda babu alamar lokacin da lamarin da zai kare. Ga abubuwan kamar haka:

▪jami’an tsaron Nijeriya sun yi karanci, ta  yadda sun  yi  kadan su iya yakar matsalar kai tsaye, ga su ko su ‘yan ta’adda kara yawa su kai a kullum.

▪iyakokin Nijeriya bude su ke ta kowane bangare-shiyassa shiga da yawaitan makamai ga hannuwan mutane (farar hula) ya zama ruwan dare.

▪ba bu makamai na zamani; wadanda kasashen da sun ka cigaba ke umfani da su don leko asiri da gano inda maboyar  ‘yan taadda suke don a kai musu hari ayi maganin su lokaci guda.

▪Ana zargin jamian tsaro ba su son matsalar ta kare: da yawa ana zargin mafiyawancin su (musammam manya da ga cikin su) suna da hannu cikin lamari, saboda sun mai da lamarin hanyar neman kudi.

▪mutane da dama sun shiga cikin lamarin- ana samun kowane bangare na mutane cikin lamarin.

▪yawaita talauci cikin al’umma shi ke sa da yawa mutane sun fada cikin lamarin. Dalilin ko saboda tsanancin talauci da mutane su ke ciki hadi da rashin dangana.

▪chin hanchi ya zama ruwan dare, ya ma ko ma cikin jinin ‘yan Nijeriya. Shuwagabanni su na almubazzaranci da dukiyar mutane shi ke sa ‘yan kasa suke ta kara tsunduma cikin talauci.

▪mai da Sarakuna shanuwar ware: Sarakuna a Nijeriya ba su da ta cewa a cikin mulkin Kasa, ga su su ke kusa da jama’a amma ba a basu dama a cikin gudanadda mulkin Kasa ba.

▪rashin aikin yi ga matasa: rashin aikin yi ya za ma ruwan dare, wannan lamarin shi ke sa wa su daga cikin matasa ke ta fadawa cikin lamarin taandanci.

▪jin haushin gwamnati da masu hali cikin al’umma- wannan lamari shi ma ya na temaka wa sosai ga kawo rashin tsaro. Matasa da dama sun shiga cikin lamari saboda jin haushi jami’an gwamnati wanda ya samu ne saboda rashin adalci na su.

          A karshe, ya kamata ga gwamnati ta kowane irin mataki su tashi tasye su yake matsalar tsaro da gaske ayi aiki ba sani ba sabo kowa ke da hannu cikin matsalar tsaro a hukunta shi ko mai matsayi nai. Sannan kuma gwamnati ta ba da dama a dauki isassun jamian tsaro a ba su kayan aiki na zamani da albashi da alawas isashshen da zai kara mu su kwarin gwiwa don su gudanadda ayukkan su ba sani ba sabo. Haka kuma ya kamata gwamnati ta bude hanyoyi da yawa na samamma matasa ayukkan yi wanda zai hana mu su zaman banza da shiga cikin ayukkan taaddanci. Yin haka shi zai sa a sami zaman lahiya tabbatacce da kuma kwanciyar hankali da wadatar arzuki a cikin kasa.

Daga Abubakar Tukur Muhammad

07060581139/abubakartukur3@gmail.com.