Tsadar Rayuwa Ke Hana Matasa Yin Aure-------- Matashiya Amira Aliyu
Amira Aliyu, ta furta hakan ne lokacin da wasu ke muhawaran, cewa yan matan yanzu basa son auren talaka sun gommaci, su cigaba da zama a gidan iyayensu, da auren talaka, Ta ce idan ana maganar son aure ne tsakanin matasa, Maza da Mata babu wanda ke bukatar aure ruwa a jallo kamar 'yan mata, cewar Amira Aliyu Zuru. Ta ce ta yi imani da Allah matasa maza da mata suna bukatar aure amma wallahi mata sun fi bukatar aure a wannan lokacin.
Tsadar Rayuwa Ke Hana Matasa Yin Aure-------- Matashiya Amira Aliyu
Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Wata Matashiya a garin Zuru da ke jihar kebbi, ta koka matuka, ta yadda tsadar rayuwa, ke dakatar da komai musamman lamuran aure.
Amira Aliyu, ta furta hakan ne lokacin da wasu ke muhawaran, cewa yan matan yanzu basa son auren talaka sun gommaci, su cigaba da zama a gidan iyayensu, da auren talaka,
Ta ce idan ana maganar son aure ne tsakanin matasa, Maza da Mata babu wanda ke bukatar aure ruwa a jallo kamar 'yan mata, cewar Amira Aliyu Zuru.
Ta ce ta yi imani da Allah matasa maza da mata suna bukatar aure amma wallahi mata sun fi bukatar aure a wannan lokacin.
Amira Aliyu Zuru, ta shaidawa wakilin mu acikin garin Zuru cewa hakika suna da bukatar yin aure, domin raya Sunnah Manzo Allah (S A W,).
Managarciya na fatar matasa su samu abin auren da suke bukata domin kula da kansu da tarbiyarsu.