Ina Jinjina Ga Tawagar 'Yan Kwallon Super Eagles----Sanata Tambuwal 

Ina Jinjina Ga Tawagar 'Yan Kwallon Super Eagles----Sanata Tambuwal 

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya taya murna ga 'yan kwallon Nijeriya a cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce "ina jinjina ga tawagar Super Eagles bisa nuna jajircewar Najeriya da mai da hankali da juriya da 'Da'a da kuma 'kwazo a filin wasa.

"Tawagar tana burgeni da salon nuna 'kishi duk da bambance-bambancen da ke tsakanin kowa.
Ina martaba hadin kan da 'yan Najeriya ke nunawa a fagen wasan kwallon kafa a duk lokacin da kungiyarmu ke fafatawa, kuma ina addu'ar Allah ya sa hakan ya yi tasiri a kowane fanni na rayuwarmu ta zamantakewar 'yan kasa.
"Madallah da tawagar kwallon ƙafar Najeriya.
"Jinjina ga 'yan kasa ga baki daya.
"Jinjina ta musanman da nasarar zuwa wannan mataki. Ku rubanya kokari domin daukar kofin AFCON 2023 a wasan karshe!"