Bishop Kukah@70: Yakamata Tambuwal Ya Manta Da Addininsa Kan Maganar Kasa?

Bishop Kukah@70: Yakamata Tambuwal Ya Manta Da Addininsa Kan Maganar Kasa?

 

 

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci bukin zagayowar ranar haihuwar babban fada a ɗariƙar katolika Bishop Mathew Hassam  Kukah in da ya cika shekara 70.

Bukin an gudanar da shi a ɗakin taro na Ladi Kwali dake Otal na Sharaton a Abuja in da manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasa da masu wa'azi  suka halarta.
An yi amfani da taron aka tara kudi domin kafa gidauniyar cibiyar KUKAH ta dindin za ta mayar da hankali ga cigaba da tattaunawa a tare da 'yan Nijeriya a tsakanin shugabannin addinai da tsarin al'umma. 

A jawabinsa a takaice wurin bukin Gwamna Tambuwal ya bayyana Bishop Kukah mutum me mai tsoron ubangiji ya kuma bayar da gudunmuwa ga cigaban Sakkwato da Nijeriya da Afirika da al'umar duniya.
A fahimtata duk da addinin musulunci bai hana ya halarci irin wannan bukin da ya kasance mu'amala  ce wadda ana yin ta a tsakanin mabambanta addinai, kuskuren da nake ganin Tambuwal ya yi biyu ne a halartar taron, shugabantar taron da kuma fadawa Duniya wai Babban limamin coci ya kawo cigaba a Sakkwato.
A jawabinsa nake ganin Tambuwal ya fifita kasa saman addininsa domin a mahangar kasa wanda ya gina gida da makaranta da wata katafariyar coci a tsakiyar birni, yakan taimakawa mabiya addininsa ai ya kawo cigaba.

Ni kan a tsarina da addinina duk wanda ya himmatu ga yada shirka ga Allah da yada addini kiristanci a lungu da sako don tabbatar addininsa ya samu wurin zama ba kyara ko jin tsoro a cibiyar Daular Usmaniya da addinin musulunci ya kafa, lalle wannan ci baya ne aka samu kwaran gaske da yakamata a koka.
Ni kan na ji takaicin jin kalmar samar da cigaban Sakkwato da gwamna Tambuwal ya sanar BISHOP KUKAH ya kawo, bunkasa da yawaitar coci a jihar Sakkwato abin takaici ne da yin tir a tsarin addinin musulunci ba kasa ba.

Ina shawartar Tambuwal ya rika sanya addini gaba kan kasa a wasu kalamai da lamurransa.