Fatana Na  Gabatar Da Dokoki Da Za Su Inganta Rayuwa Mata da Matasa a Kano---Honarabul Halima Danbatta

Amsa: Kwarai da gaske,ai Bahaushe ya yi magana yace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,don idan Mata suna cikin wata matsala na bata shiga matsalar,ko zan shiga,in ni ban shiga ba 'ya ta za ta zo ta shiga wannan matsalar, saboda duk abinda ya ke zagaye da Mata ko'ina a Duniya na su ne hakan  ya sa aka ce ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, don duk abinda na ji kin ji shi, kawai dai ace banbamcin launin fata ne, canjin wuri dama ce aka samu na samun taimakon, Asibiti,Tituna,Ruwan mai kyau na Sha,wutan lantarki,mu'amalar rayuwa ko samun saukin rayuwa, da dai sauransu shi ne ya sa na nace bari na shigo naga irin gudumawar da zan iya bayarwa al'umma nima.

Fatana Na  Gabatar Da Dokoki Da Za Su Inganta Rayuwa Mata da Matasa a Kano---Honarabul Halima Danbatta
 
 
 

Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna

 

 

Hajiya Halima Zubairu Abdulhamid Danbatta, 'yar takarar  kujerar Majalissa ce a karkashin Jam'iyyar PDP A Mazabar Danbatta,a karamar hukumar Danbatta dake jihar  Kano,ta ce in Allah ya bata wan nan  Kujerar  zata mayar da hankali ne Kan Kawo kudorori da zasu taimaka wajen inganta Rayuwar Mata da Matasa, kasan cewar sune keda bukartar mutukar kulawa a cikin al'ummar a Tattaunawarta da Abdullahi Alhassan,a Kaduna yayin wani taro da reshen Mata na majalisar dinkin duniya ta tara mata yan takar a kujeru daban- daban don horar da su yarda ake yakin neman zabe dama harkokin zaben a Kaduna.

 
Tambaya: ko zamu ji dan takaitaccen tarihinki?
 
Amsa: An haifeni a jihar Kano,kuma nayi Makaranta a Kano Capital School,kuma nayi kararu a jami'ar Bayero dake Kano da kuma Dangote Business school dake Kano,bugu da kari ni yar kasuwa ce,haka kuma ni mai rike da Kungiyace mai zaman kanta dake tallafawa Mata da Matasa don su zama masu dogaro da kansu cikin al'umma.
 
Tambaya: Me yaja hankalinki shiga harkar Siyasa?
 
 
Amsa:To abinda ya shigar dani shine lna abubuwan kungiyoyi kuma ya hada da  abinda kungiyoyin duniya,to kuma na shiga Danbatta don in kafa nawa kungiyar na taimakawa Mata da Matasa,to sai ya Matan da na fara haduwa dasu lna gogaiya dasu cewar ya suke sarrafa matsalolinsu ya suke cinikaiya tsakaninsu don lta kungiyar tawa Kan cinikaiya ce,wato Entrepreneur,a turance,koyar da Sana'a don dogaro da Kai kenan,kuma yarda zaka koyar da Sana'oi to sai naga kungiyoyin nan kuma naga Mata da yawa suna Sana'oi kalala ,kuma har sun hada kansu,suna da kungiyoyi to kuma sai naga kungiyoyin nan ya kamata a bunkasa su kuma a tallafa masu yarda ya kamata,garin yin haka lnata dan kokarina mutane da Mata muna ta abubuwan kungiyoyi sai suka bijiro da cewa suna son in shiga Siyasa sai nace musu ni ba yar Siyasa bace,lna dai cinikina ne  lna abubuwan kungiyoyi ne kawai sai sukace aibanbancin Siyasa da kungiya ai kadan ne,San nan su kuma suna  ganin lna kwatanta adalci kuma ba'a taba ba Mace ba,sukayi ta naci cewa laile na fito takarar kujerar Majalissa mai wakiltar Dabatta din,na zauna nayi tunani Shine na fito,da yake lnata hudda dasu lnata ganin matsalolinsu shine da abinda yakamata a tallafawa,kaga ga gwamanatin tarayya data jiha ,sai naga al'ummar Danbatta basa cin muriyar sa,sai kaga to me yake jawo haka? nayi bincike naga to ldan kana kokari a naka matsayin naka lya taimakawa mutum biyar, in ka shiga gwamanati zaka taimakawa mutum dubu,to saboda haka naga duk mutumin da yake taimakon al'umma , saboda ba wai don Karan kanka  bane don al'umma ce to ka fitar da al'umma da kake ciki ka gyara al'umma da aketa samun matsala a ciki ya za'a ce a kalli Kano tafi ko lna mutuwar Aure,da Zaurawa da fyade, duk wan nan abubuwan harda cin zarafin ya Mace,ya za'a ce an kawo a yanke hukuncin cewa adauki tsastsauran mataki Kan fyade,wai anyi wasa dashi da shi fyaden nan fa za'a lya yiwa yarka fa,kanwarka fa,da matarka ko yarka, to in ba'a kafa dokar tsare ya Mace ba,a Musulunci ma kanada lada,to sai nagama wasu dokokin ma yakamata mu shigo ciki dumu-dumu don muna da dama,rashin Mace ne ,dan ance cutar Mace na ya Mace ne,shi yasa nace Bari in na fito naga damar da nake dashi na gwada don mutaimaki  al'umma.
 
Tambaya:In na fahimce ki sanin matsalolin su ne yasa kika shiga neman takarar kenan don kina ganin za'a lya shawo Kan matsalolin ta hanyar kawo kudurori ko  dokokin da suka kamata?
 
Amsa: Kwarai da gaske,ai Bahaushe ya yi magana yace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,don idan Mata suna cikin wata matsala na bata shiga matsalar,ko zan shiga,in ni ban shiga ba 'ya ta za ta zo ta shiga wannan matsalar, saboda duk abinda ya ke zagaye da Mata ko'ina a Duniya na su ne hakan  ya sa aka ce ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, don duk abinda na ji kin ji shi, kawai dai ace banbamcin launin fata ne, canjin wuri dama ce aka samu na samun taimakon, Asibiti,Tituna,Ruwan mai kyau na Sha,wutan lantarki,mu'amalar rayuwa ko samun saukin rayuwa, da dai sauransu shi ne ya sa na nace bari na shigo naga irin gudumawar da zan iya bayarwa al'umma nima.
 
Tambaya: Ko akwai wani abu da kike shirin yi ldan Allah ya baki wan nan Kujerar da ni ban tambaye ki ba?
 
Amsa:Kasan aiyukan dan Majalissa guda uku ne,na farko gyara dokoki da kafa Sabbin dokokin,na biyu Bibiyarsu dokokin,sai na uku yin aiyukan mzabu, sune ummul aba'isin aikin ka a matsayin ka na dan Majalissa jiha to kuma wan nan  abin in basu kawo ba,sune zasu lya gyara rayuwan dan Adam,sai Makaranta ko ta gwamanati ce da take an riga  ginata su samu  karin ajujuwa  koda goma ne ko baka gina sabuwa ba, saboda wani wurin suna bukatar Karin ajine ba wai ginin sabuwa ba kawai inganta ake dasu  inda babu kuma sai ka gina musu wata sabuwa kaga ka taimakawa al'umma da kake wakiltar ta hanyar samar musu da Makaranta wanda yana cikin abunda zan mayar da hankali ldan Allah ya bani wan nan Kujerar.
 
San nan kuma zancen su Tituna yan kauce ko ince mazauna karkara keda bukatar haya don fitar da amfanin noman da sukayi zuwa birane, akwai inda zaka ga rairayi ne ,da keda bukatar yin wasu da fadada hanyar don sauwake musu wahalhalun da suke fama dashi.
 
Haka kuma akwai  bangaren lafiya,ya kamata ariga ragewa manyan asibitoci nauyi,wato general hospital kenan,da kuma Asibitin koyarwa ta hanyar Gina kananan asibitoci musammamma a yan kunan karkara duk lungu na da sako wanda in mace ta tashi na kuda za'a kaita chen, basai anta ciwon Kai ba cikin dare ko asiba ba,ko rashin mota ko mashin da zai kaita chen ba,yar za'ayi taje chen,shi yasa aketa samun mutuwar jarirai yake yawa, San nan kuma ba ko wani ciwo bane zaka lya zuwa chen nesa ba, kananan asibitocin nan duk zasu lya yi mana maganinsu,kaga wan nan aiduk cigabane.
 
Bugu da kari abubuwan dai da dama Matasa da za'a kakkakafa su nan kusa yanda matashi zai tashi da safe in ya tashi yasan inda zai je,kuma yasan rayuwan tasan inda ta dosa.
 
Tambaya: Daga karshe wani Kira kike da shi get Al'ummar Danbatta wanda kike da fatan wakiltar su in Allah ya baki dama.?
 
Amsa: lna Kira ga al'ummar  Danbatta dama Jihar Kano baki daya su zabi chenchenta kada subi kudi lokacin da za'a baka kudi don Kai zabe ya wuce,
Haka kuma lokacin da zaka saida kuriar ka ma ya wuce ldan ka duba cewa dan abinda ake baka kwana nawa zai yi ya kare ? amma in ka zabi wan ya chenchenta zai kawo maka abubuwan cigaba a yan kunanku.