Yakamata Gwamnan Sakkwato ya dubi Malamai da ma'aikatan lafiya
Tsohuwar Gwamnatin Sakkwato ta Sanata Aminu Waziri Tambuwal ta dauki ma’aikatan lafiya da suka dade suna aikin sadaukarwa ga gwamnatin jiha, ganin wahalar da suka sha da kuma bukatar da ake da ita ta ma’aikatan, gwamnati ta dauke su aiki da zimmar zata fara biyansu albashi daga watan Mayun 2023, rashin samun sukunin yin albashi ga ma'aikatan jiha gaba daya ya sanya ba su ci gajiyar fara biyan su ba. Ma'aikatan hankalinsu a kwance ganin gwamnatin da za ta gadi Tambuwal, ko ba'a yi daukar ba da sun zo ba za su bari lamari ya tafi ba ma'aikata, balle ma an sauwaka masu albashi ne kawai za su fara biya, sai gashi shiru har yanzu ba a fara biyan ba sama da wata bkwai a yanzu.
Malaman makaranta da suke da karanci sosai a makarantun jihar, ganin yadda mutane suka dauki aikin karantarwa aikin jiran aiki, su ma tsohuwar gwamnati ta dauke su aiki an ba su takardun kama aiki tare da sanar da su za a fara biyansu albashi kafin a tura su makarantun da za su rika koyarwa, suna cikin jiran albashhi ne gwamnati ta kare, wasu daga cikin wadanda aka dauka aikin sun yi farincciki da haka, domin suna son gwamnatin da suka zaba ce za ta fara biyansu albashi, kash sai gashi gwamnatin ta saka musu da dakatar da daukar da aka yi musu ba tare da sanin makomarsu ba.
Ma'aikatan gwamnati da za su yi aiki a ofisoshi su ma dai haka tsohuwar gwamnatin ta cika hannu da su, domin ta yi la'akari da yanda ake da gibi sosai a ma'aikatu domin mutane suna yin ritaya amma ba a dauki madadinsu ba tsawon lokaci, a haka gwamnatin ta dan watsa wasu ma'aikatan don a dan farfado da aikin gwamnati, su ma kamar sauran ba a fara biyansu ba, gwamnati mai ci yanzu ta Dakta Ahmad Aliyu Sokoto bayan kwamitin da ta kafa da zai binciki lamarin, a yanzu gashi wata takwas ba a ce masu ga matsayar su ba, an bar su da takardar samun aiki ba a gaya masu an soke daukar ba, kuma ba a fara biyansu albashi ba.
Yakamata gwamnatin Sokoto mai ci a yanzu karkashin Gwamna Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya dubi mutanen nan da idon rahama ya sanya su cikin tsarin biyan albashi domin samun cigaban jiha ta hanyar rage marasa aikin yi.
Kyale wadannan mutane da ke da muhimmanci a cigaban jiha bai dace ba akwai bukatar gwamnati ta sake tunani ta shigo da wadan nan mutane cikin tsarin gwamnati domin kawo sauyi mai ma'ana ga al'ummar jiha.
Daga Muhammad Namanu Tudun Wada.