Yakamata Hukumomi  Su Duba Halin da Al'umma ke Ciki a Nigeriya

Yakamata Hukumomi  Su Duba Halin da Al'umma ke Ciki a Nigeriya

Daga Fatima Bilal Abubakar Galadanci

Gaskiyar magana ya kamata 'yan siyasar mu su duba halin da al'umma su ke ciki,
Domin idan aka duba za'a ga cewa komai ya taɓar-ɓare, ga yajin aiki  ga Jami'o'in ƙasar nan, ga mawuyacin hali da al'umma ke cikin na rashin abinci,

Ga kwacen waya da matasa ke yi da ya zama ruwan dare musamman a wannan Gari na mu na  Kano,

Su kuwa ƴan mata wasu sukan bi samari dan samun abin duniya, don haka nake kira ga matasa da su zauna lafiya,

I ta kuwa gwamnati da masu hannu da shune a taimawa matasa don ganin an fito da su daga halin da suke ciki.

hanyoyin da zaa bi don taimakawa matasa su ne ta hanyar kasuwanci ba sai aikin  Gwamnati ba, hakan shi ya haifar da rashin tsoro a zuciyarsu har su ke shiga abubun da ba su kamata ba na  yin kwace da sauransu,

Don haka, halin matsi da  kuncin rayuwa ya sanya  zuciyar matasa ta kekeshe kwata kwata ba tsoro a tattare da su, saboda ahalin da suka shiga ya zamana ba sa tsoron kowa,ko kuma suna abin da suka ga dama , don haka nake kira da  dan Allah a taimaka wa matasa da aikin yi da sana'o'i da sauransu, da haka ne za ka ga sun zauna lafiya, arziki da wadata  su ƴaɗu a cikin bar al'umma.

Fatima ta rubuto ne daga Kano,  

email: fatimabilalabubakar2020@gmail.com