Kashe Mutane Da 'Yan Bindiga Ke Yi Abu Ne Mai Tayar Da Hankali Da Taɓa Zuciya

Kashe Mutane Da 'Yan Bindiga Ke Yi Abu Ne Mai Tayar Da Hankali Da Taɓa Zuciya

Daga Abbakar Aleeyu Anache, 

Hakika akwai rashin imani irin yadda bata gari ke bude wuta, kan Fararen hulla, da jami'an tsaro, suna tsaka da neman samun zaman lafiya da Kwanciyar hankalin al'umma.

Tabbas labarin mummunan harin da ake  kaiwa jami'an tsaron Najeriya a jihar Borno inda aka kashe Sojoji abin takaici ne matuka.

Ina mika sakon ta'aziyya ga al'ummar jihar Borno da rundunar sojojin Najeriya da gwamnatin Najeriya, da kuma iyalan wadanda abin ya rutsa da su.

Ina kara jaddada kira na ga jami'an tsaro su, kara zage dantse, domin shawo kan wannan matsala ta, tsaro.

Sannan ina jaddada kira ga al'umma su rika taimakawa hukumomin tsaro da muhimman bayanai domin katse yunkurin 'yan ta'adda. 

Ina da yakinin cewar Najeriya za ta yi nasara da karfin ikon Allah.