Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Ya Sayi Fom Na Neman Shugabancin APC

Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Ya Sayi Fom Na Neman Shugabancin APC
 

Kungiyar Support A.A Yari for National Chairman ta sayi Form na takarar Shugaban Jam'iyar APC ga Shugaba  Abdulaziz Yari Abubakar (Shatiman Zamfara), Tsohon Gwamnan Zamfara kuma Tsohon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya akan Kuɗi Naira Miliyan 20, karkashin jagorancin Engr. Abdullahi Tsafe (chief of Staff) da Senata  Tijjani Yahaya Kaura da kuma Shugaban Ƙungiyar Engr. Dan Baba Kaduna (National President)

 
Malam Abdulaziz Yarin yana Ƙasar Saudiya inda zai gudanar  da ibadar Umrah kana daga bisani zai dawo ƙasa Najeriya domin cigaba da gudanar da muhimman ayukkansa kafin ranar 26/3/2022 da za'a gudanar da Taron Kasa na APC
Kamar yadda aka sani tsohon gwamnan ya nuna sha'awar tsayawa takarar kujerar domin ya kawo sauyi mai alfanu a jam'iyar.
Tun kafin sayin fom da yawan mutane sun san da wannan kudirin nasa, a yanzu kuma an tabbatar da kudirinsa ciyar da jam'iya da kasa a gaba.
ABUBAKAR S. LIMANCHI