Salame Ya Yarda Da Shugabancin APC Na  Isah Achida?

Salame Ya Yarda Da Shugabancin APC Na  Isah Achida?

Honarabul Abdullahi Balarabe Salame dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a jihar Sakkwato ya halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC wanda shugaban jam’iyar Alhaji Isah Sadik Achida ya yi  gayyata a ranar Laraba.

Halartarsa taron ya zo da bazata kwaran da gaske  da yawan mutane na  danganta  zuwansa dole akwai magana har wasu na tambayar ko Salame ya yarda da shugabancin Isah Sadik Achida ne a yanzu.

Yayinda wasu ke danganta zuwansa bai da alaka da yarda da shugaban jam’iya domin harka ce ta jam’iya ta taso shi ne ya halarta.

Wasu na ganin a fakaice ya aminta da shugabancin ne tun da har za a gayyace shi taro ya aminta ya zo a karkashin shugabancin da bai aminta da shi ba a farko.

Salame tun bayan zaben shugabanin jam’iya ake jayayya da shi kan wanda zai jagorancin jam’iyar a matakin jiha da kananan hukumomi  da mazabu, kwatsam sai gas hi ya halarci taron da wadanda yake jayayya da su suka kira, shin ko ba yukarsa ne zai mayar kube ba.

Taron na masu ruwa da tsakin duk da kalaman Salame sun tayar da hazo a wurin zaman a karshe dai an watse taro lafiya.