Yakamata Gwamnati Ta Tallafawa ƙungiyoyin Da Ke Horar Da Mata Da Matasa Sana'o'in Hannu

Shugabar gidauniyar Zarah and Arthur, Hajiya Zarah I. Abdullahi tayi kiran a lokacin bude shirin horar da mata dari sana'o'in hannu a Minna. Ta cigaba da cewar tun fara wannan shirin da muka fara kyauta wanda muna da kudurin cigaba da aiwatar da shi, ba hannun kowa ko tallafin wani, mu ne muka dacewarsa muke daukar dawainiyarsa. Burin za mu cigaba da wannan shirin ta yadda muna tunanin horar da mutane dubu biyar daga yanzu zuwa shekarar 2023 idan Allah ya ba mu ikon hakan. Sau tari gwamnati na bada tallafin kudade ga jama'a dan yin sana'a, amma saboda rashin kwarewa da rashin sanin yadda za a juya kudaden sai ka ga kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, saboda tallafin ana bada shi ba tare tantancewa ba, idan gwamanti zà ta janyo kungiyoyi irin na mu a cikin sai ka ga tallafin na zuwa inda ya dace.

Yakamata Gwamnati Ta Tallafawa ƙungiyoyin Da Ke Horar Da Mata Da Matasa Sana'o'in Hannu
Daga Bàbangida Bisallah, Minna.
 An nemi gwamnati da tà rikà taimakawa kungiyoyin da ke daukar dawainiyar horar da mata da matasa sana'o'in hannu, hakan zai karfafa masu guiwa ta yadda za a taumakawa jama'a dan samun madogarar rayuwa.
Shugabar gidauniyar Zarah and Arthur, Hajiya Zarah I. Abdullahi tayi kiran a lokacin bude shirin horar da mata dari sana'o'in hannu a Minna.
Ta cigaba da cewar tun fara wannan shirin da muka fara kyauta wanda muna da kudurin cigaba da aiwatar da shi, ba hannun kowa ko tallafin wani, mu ne muka dacewarsa muke daukar dawainiyarsa. Burin za mu cigaba da wannan shirin ta yadda muna tunanin horar da mutane dubu biyar daga yanzu zuwa shekarar 2023 idan Allah ya ba mu ikon hakan.
Sau tari gwamnati na bada tallafin kudade ga jama'a dan yin sana'a, amma saboda rashin kwarewa da rashin sanin yadda za a juya kudaden sai ka ga kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, saboda tallafin ana bada shi ba tare tantancewa ba, idan gwamanti zà ta janyo kungiyoyi irin na mu a cikin sai ka ga tallafin na zuwa inda ya dace.
Dan haka muna godiya ga gwamnati nà ba mu 'yancin tafiyar kuñgiyoyin mu ba tare da samun tsangwama ba, domin da ba a tantance an ba mu takardar amincewa mugudanar da kungiyoyin mu ba, da ba mu samu damar baje kolin ilimin ga jama'a dan su anfana ba.
Ina kiran Iyaye mata da babban murya da suka amince su bada lokacinsu dan koyon sana'a duk da harkokin gida da ke gaban su, da su mayar da hankali akan abinda suka zo koya, lokacin da zasu fara cin moriyar abinda aka koyar da su ba ma kusa.