“APC Ba Zaɓi Ba Ne A Gare Ni” — Natasha Akpoti Ta Yi Watsi da Kiran Sauya Sheƙa

“APC Ba Zaɓi Ba Ne A Gare Ni” — Natasha Akpoti Ta Yi Watsi da Kiran Sauya Sheƙa

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana karara cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba zaɓi ba ce a gare ta, tana mai jaddada cewa ba ta da niyyar bin sahun masu sauya sheƙa ko amincewa da kowanne irin matsin lamba ko rarrashi na siyasa.

A wata sanarwa da ta fitar, Akpoti ta ce an tuntube ta daga wasu mutane da ke kusa da fadar shugaban ƙasa Domin ta koma APC, amma ta yi watsi da tayin, tana mai cewa ba za ta yarda a tilasta mata ko a ruɗe ta da alkawuran siyasa ba.

Wannan mataki na Sanatar ya sake tayar da kura kan yawaitar sauya sheƙa da ke gudana a fagen siyasar Nijeriya, musamman daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar mai mulki.

Masu sharhi na ganin wannan matsayar ta Akpoti na nuna tsayuwarta kan ra’ayi da kuma ƙudurin ci gaba da bin tafarkin siyasar da ta yi imani da shi, ba tare da la’akari da matsin lamba daga manyan masu ruwa da tsaki ba.

KBC Hausa