Kafa Kwamitin Bincike: APC da PDP  Sun Sa Zare a Sakkwato 

Kafa Kwamitin Bincike: APC da PDP  Sun Sa Zare a Sakkwato 

Tun lokacin da sabuwar gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Dakta Ahmad Aliyu ta dare kan karagar mulki aka fara samun takon saka a tsakanin bangaren gwamnati da babbar jam’iyar adawa ta PDP,  tana ganin kamar ana yi mata bita da kulli ne a wasu tsare-tsare da gwamnati ta fitar,  musamman soke duk wani mataki da tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya zartar kwana daya da kammala zaben Gwamna a watan Maris 2023  har zuwa karshen wa’adinsa da yak are Mayu 2023.

Soke  nadin  sarautun da gwamnatin baya ta yi dana  manyan sakatarorin da daraktoci, in da  gwamnatin ta kafa kwamitoci kusan biyar don sake duba wasu aiyukka da aka zartar a lokacin Tambuwal hakan  ya kara ruruta wutar hamayya a tsakanin bangarorin biyu.

Ba a kare da wannan ba sai a satin nan gwamnati ta kafa wani kwamitin mutum biyar na manyan masana shari’a da ya kunshi tsohon Alkali da lauyoyi  da zai duba muhimman abubuwa biyu da gwamnatin Aminu Tambuwal  da ta gabata ta aiwatar.

A wata sanarwa da Sakataren yada labarai na gwamnan Sakkwato  Alhaji Abubakar Bawa ya fitar ya ce gwamna ya aminta da kafa kwamitin korafi  da zai binciki yanda aka yi gwanjon kayan gwamnati da yanda aka raba filaye da sauran abubuwa da kuma yadda aka sayar da gwanjon gidajen gwamnati wanda gwamnatin(Tambuwal)  ta yi.

A cewarsa kafa kwamitin na mutum biyar karkashin jagorancin Alkali(mai muabus)M. A Pindiga, Jacob Ochidi da Alhaji Usman Abubakar da Lema Sambo Wali  mambobi ne a kwamitin yayin da Nasiru Mohammed Binji yake sakataren kwamiti, yin haka na cikin damar da kundin  dokar Sakkwato ta 1996 sashe 1(2) ta bayar na kafa kwamitin korafi irin wannan in bukatar hakan ta taso.

Abubuwan da ake bukatar kwamitin ya aiwatar guda biyu ne na farko ya zakulo dukkan kayan gwamnati da aka sayar ko yin gwanjon su da suka hada da dukkan ababen hawa na gwamnati a matakin jiha da kananan hukumomi da kadarorin gwamnati, su kuma kididdigi asusun ajiya na gwamnati don sanin yawan kudin da aka samu da aka yi gwanjo ko aka sayar da kadarorin gwamnati. Na biyu a samu bayani kan filayen gwamnati a jiha don sanin filayen da aka baiwa daidaikun mutane da kungiyoyi da sanin dukkan gidajen gwamnati da aka sayar ko yin gwanjonsu.

Gwamnan  ya baiwa kwamitin wata biyu ya kara aikinsa daga lokacin da suka yi zaman farko tare da gwamnan.

Shugaban jam’iyar PDP a jihar Sakkwato Honarabul Bello Aliyu Goronyo ya zargi gwamnati da musguna masu ne take yi kuma za su jure dafin lamarin don haka suke fadin abin da gwamnatin Ahmad Aliyu take yi masu wand aba daidai ba ne.

“Mutanenmu da aka  ci ma zarafi sun hada da kwamishinoni da shugaban ma’aikatn fadar gwamnati a mulkin Tambuwal da dan takarar gwamna a zaben 2023 a jam’iyarmu ta PDP da tsoffin shugabannin kananan hukumomi,” a cewar Bello  Goronyo.

Ya ce kwamitin da gwamnatin APC ta yi domin ya sake duba yanda aka yi gwanjon kadarorin gwamnati an yi ne bayan da wasu bata gari sun ci zarafin mutane.

“Muna sane da yanda ake kokarin kwace wa mutanenmu ababen hawa da aka yi masu gwanjo abin da ake yi cin zarafi ne, yi wa mukaraban gwamnati  gwanjo ba sabon abu ba ne da aka fara a gwamnatin Aminu Tambuwal, Bafarawa da Wamakko duk sun yi hakan.” In ji Goronyo.

Ya yi  kira da mambobinsu da su yi tsaye wurin kare mutuncinsu da walwalarsu da lafiyarsu duk sanda hakan ya taso.