Magoya bayan NNPP 6 sun rasu a haɗarin mota yayin da Kwankwaso ya ziyarci garin Lafia 

Magoya bayan NNPP 6 sun rasu a haɗarin mota yayin da Kwankwaso ya ziyarci garin Lafia 

 

Wasu magoya bayan jam'iyar NNPP sun rasu a garin Lafia, Jihar Nasarawa a yau Lahadi.

 
Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin ya faru ne lokacin da kan motar da su ke ciki, wacce take kan jerin-gwanon motoci na Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ƙwace.
 
Motar da ta yi haɗarin na cikin ayarin ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Kwankwaso, lokacin da ya je Lafia domin ƙaddamar da ofishin jam'iya na jihar.
 
Rahotanni sun bayyana cewa da yawa daga cikin waɗanda su ke cikin motar sun samu raunuka daban-daban.