Gwamnatin Sakkwato ta sayawa kowane kwamishina motar miliyan 58?

Gwamnatin Sakkwato ta sayawa kowane kwamishina motar miliyan 58?

 
Gwamnatin jihar Sakkwato  ta kashe kudi biliyan 1.764 wurin sayen motoci 30 da za a baiwa mambobin majalisar zartarwa ta jiha a watanni uku na farkon shekarar 2024.
Jaridar SolaceBase ta fitar da bayanin tare da kawo hobbasar gwamnati a kasafin kudin shekarar don an karar da jama'a tafiyar gwamnatin Sakkwato.
A bayanin sun ce kowane Mamba a majalisar zartawa ta jiha zai samu mota da kudinta zai kai naira miliyan 58.
An sawo motocin ne a lokacin da ake ta kira ga gwamnatoci su rage yawan kudin da suke kashewa saboda matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Nijeriya, halin da Sakkwato ma tana ciki.
A bayanin sun nuna Gwamnati  a gefen Noma miliyan 45 ne kadai ta kashe, a ma'aikatar ilmi manyan aiyukkan da aka yi miliyan 14 aka kashe a wata ukun na farkon shekarar 2024.