Buhari Ya Yi Kira Ga Mutanen Nijeriya Su Zabi Tinubu

Buhari Ya Yi Kira Ga Mutanen Nijeriya Su Zabi Tinubu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wata sanarwa da ya fitar Lahadi  wadda ya sanyawa hannu da kansa ya roki mutanen Nijeriya da su zabi dan takarar shugaban kasa da jam'iyarsu ta tsayar waton Bola Tinubu.

Buhari ya ce zan yi amfani da wannan damar na gode wa masu zabe da suka zabe ni matsayin shugaban kasa a zango biyu.
"Bana takara a wannan zaben amma dai jam'iyarmu ta APC ta tsayar da Bola Tinubu kamar yadda na fadi a baya mutm ne mai son cigaban kasarmu  da mutanenta.
"Don haka ina kira gare ku da ku zabi Tinubu abin amincewa ne na yarda zai kawo cigaba,"a cewar Buihari.
Kan maganar halin da ake ciki Buhari ya ce yana sane kwarai kan matsain da ake ciki saboda wasu tsare-tsaren da gwamnati ta kawo wanda take son ciyar da kasa gaba.
Ya baiwa mutanen kasa hakuri ana daukar matakai na ganin an samar da saukin wahalar da ake ciki, da yardar Ubangiji za a samu mafita a halin da ake ciki.