KANWATA: Fita Ta Uku

KANWATA: Fita Ta Uku


  KANWATA

    Na
Jiddah S Mapi

   *chapter 3*

    ~"aa Amrah idan kika cire anko yanzu ai zaiyi wuri kibari idan ansa date saiki cire ko?"
Amrah tace "no yau zan cire domin zamu kece raini sabida kawayena 'yan wanka ne kuma 'yan karya, kinga gara nacire musu da wurin"
Fadila tace "shikenan idan hakan zaisaki farin ciki ni ai banida matsala"
Dariya Amrah tayi tace "shiyasa nake sonki kamar yanda kema kike sona"
Dariya kawai Fadila tayi.

     "Bayan mangarib saiga iyayen Kamal sunzo ansa date sati uku masu zuwa insha Allah, Fadila ce kwance a d'aki ta d'aura kanta a pillow tana tunanin Kamal, ganin tunanin bazai kareba yasata d'aukan waya ta kirashi, ringing biyu ya kashe saiga kiranshi yana shigowa, ajiyar zuciya ta sauke tanjin wani irin sonshi yanabin duk jikinta, d'aukar wayar tayi cikin sanyin muryanta tace "hello"
Kamal Wanda yake zaune a d'akin Umma ne yace "Fiancy tin d'azu nake tunaninki ji nake kamar lokacin da akasa mana yayi nisa, Wallahi ina matukar bukatarki kusa dani, sau da dama idan naje wurinki muna fira ni kad'ai nasan yanda nakeji a jikina, please fiancy ki fad'awa su Mama a rage kwanakin nan, kinji"
Ajiyar zuciya Fadila ta sauke itama yanda takejin son Kamal a zuciyarta ji takeyi kamar lokacin Aurensu yayi mata nisa, to Amma ta yaya zata fara yiwa Mama wannan maganar?
"Kinyi shiru, fiancy"
Firgigit ta dawo daga tunanin da take, cikin muryanta me sanyi tace "Kamal gobe fa yana saurin zuwa, yanzu zakaga ranar Aurenmu tazo kamar da wasa, Dan Allah ka kara hakuri sannan ka yawaita yin Azumi da fad'in astaghfurullah insha Allah zaka samu sauki, gaggawa fa aikin shaid'an ne"
Da haka sukaci gaba da firansu tana kara kwantar mishi da hankali, sai kusan karfe goma kafin suka hakura kowa yakashe wayarshi dukkanninsu sunajin soyayyar d'an uwansu a zuciyoyinsu, musamman Kamal dayake jin kamar Fadila itace rayuwarshi idan babu Fadila yana ganin shi poster ne bashida anfani, tashi yayi daga d'akin Umma ya tafi d'akinshi, kwanciya yayi tareda janyo filo ya rungume a hankali ya lumshe idonshi yanajin soyayyar Fadila yana kara shiga cikin kirjinshi, 
Fadila kuwa suna gama wayar tashiga band'aki tayi Alwala, sallah raka'a biyu tayi kafin ta hau gado ta kwanta a gefen Amra wacce ta zage tun d'azu tana chatting a WhatsApp da kawayenta, suna maganar irin d'inkin da zasuyiwa zanin ankon su, Fadila ce ta wupce wayar a hannunta tana dariya ta b'oye a karkashin filo, Amrah waro manyan idanunta tayi ganin an wupce wayarta, da sauri ta tashi tana kwatan wayar a hannun Fadila, Fadila sai dariya take tana cewa "yaufa bazan baki wayarnan ba so nake muyi fira"
Amrah tana kokarin kwace wayar suka fara damben wasa Amma Fadila tafi karfinta, saida Amrah tayi laushi ta gaji da kwatan wayar yasa tace "Haba my sister nasan zaki bani, Dan Allah kiyi hakuri wallahi message d'aya zan turawa Zee sai in baki"
Fadila waro manyan idonta tayi itama tace "Amrah har yanzu baki daina Kawance da yarinyarnan ba? Kinsan fa ko Mama batason yarinyar batada kunya ko kad'an"
Amrah tace "wallahi nikama na rabu da ita shine tazo tacemin wai ta tuba ta daina bibiyar maza inyi hakuri muci gaba da kawance, shine tabani tausayi shiyasa na yadda muka koma kawance"
Fadila shiru tayi tana nazarin maganar kanwar tata, to Amma tasan Amrah bazatayi mata karya ba, "shikenan ba komai indai ta shiryu ai ba komai kici gaba da bata shawarwari ta gyara rayuwarta"
Amrah murmushi tayiwa Fadila Wanda ya bayyanar da dimple nata, itama Fadila mayar mata da murmushi tayi Tamika mata wayar cikin sakin fuska.

    "Washe gari wata matace wacce suke kira da unty Sadiya  (Unty Sadiya Ta d'auki Amrah da Fadila kamar kannenta wanda suka fito ciki d'aya, saidai tafi shiri da Fadila sabida hakurinta, Unty Sadiya tanada miji da yara guda biyu, Aisha da Nabil, tana garin Yola itama a unguwar Jambutu)
Itace tazo domin duba su Fadila da Amrah, ganin Unty Sadiya ba karamin murna sukayi ba domin duk lokacin datazo saita koya musu girki sannan tabasu shawarwari, itama murnar ganinsu tayi, shiga tayi suka gaisa da Mama tace "to tinda mun gaisa da mama sai kuzo muje d'akinku domin yau akwai lecture"
Mama kallonsu tayi tace "aikin kenan dama sai kuje kuji dashi"
Dariya sukayi gaba d'ayansu suka tafi d'akinsu, d'alewa gado sukayi Amrah ta saki kunnuwa ta zubawa Unty Sadiya ido tana jiran taji bayani, unty Sadiya tace "Amrah yau fa ba maganarki bace, Maganar Amare ne, sabida ita Fadila ta kusan Aure kinsan saida lectures"
Amrah had'a rai tayi tace "wallahi babu inda zani saidai a fad'i komai a idona"
Fadila ganin idan Amrah batanan kamar ran Amrahn zai b'aci yasa tace "Unty Sadiya ai Amrah ma wata rana zata zama Amarya ko?"
Dariya Unty Sadiya tayi tace "hakane to inaso Ku bud'e kunnuwanku kujini da kyau, musamman ma ke Fadila keda kike shirin shiga d'akin miji"
Gyara zama sukayi sukace "muna jinki Untyn mu"
Unty Sadiya tace "da farko zan fara yi muku bayanai akan girke girke".

     *Girki*

   "shi wannan girki da kukeji ana fad'a bawai ki d'ibo ruwa ki hura wuta ki dafa abinci ake nufi ba, idan ance girki ana nufin ki kwantar da hankalinki kiyi girki me dad'i Wanda duk Wanda ya d'ana Saiya tambaya wayayi girkin nan, ki kasance kin iya sarrafa abubuwa da dama da kanki, girki yana daga cikin abubuwan da yakesa miji yaji yana kara son matarshi, ya kasance kin iya girki na gargajiya da kuma na zamani, shi girki na zamani wani lokacin zaki iya kirkiran Abu da kanki kiyi kuma kiga yayi dad'i, ki kasance kin iya snacks da kuma yin drinks da kanki kamarsu (banana juice, Apple juice, Mango juice, da sauran kayan itatuwa) su wad'annan anaso yazamana kinada blander abun zaizo miki da sauki, ki kasance idan kinji ana maganar girki to kiyi kokari ki koya kuma ki gwada da haka ake kwarewa"
Sai kuma Abu na biyu, shine.

    *Tsafta*

  "Shi tsafta abune me girma idan kinada tsafta to komai zaizo miki da sauki, ki kasance kin iya tsaftace jikinki da kuma gidanki sai uwa uba yaranki"
Sai Abu na Uku shine.

   *iya magana*

  "Wallahi rashin iya magana yana kawo rashin zaman lafiya a tsakanin kawaye ma balle mata da miji, idan kazauna da wasu mutanen zakaji sun shiga zuciyarka meyake kawo hakan? Shine iya magana, wasu mutanen kuma idan kuka zauna dasu maganar dazai fito a bakinsu wane maganar dabbobi tsabar rashin iya rashin magana, an samu wani mutum a zamanin Annabi Muhammad (S A W)
Mutumin yanada rowa sosai, sai ranar yana zaune a wani wuri yanacin (Tufa) Apple kenan, wasu mutane sukazo wurin sukace kad'an mana, mutumin yarasa yanda zaiyi sai yace, ana rabawa a gidan sarki, mutanen dasukaji haka sai suka kwasa da gudu sai gidan sarki, shima ganin sun tafi yasashi wani tunani yace kai karfa suje kuma abasu da gaske, shima kawai saiya bisu da gudu, suna zuwa sarki yace me yake faruwa? Sukace wai aance ana raba Tufa a gidanka, shikuma sarki ganin yafi karfin yace ba'a rabawa sai yasa fadawa suka fara raba musu, shima wancan marowacin saida ya samu, to kunga anan ai iya maganar shine ya jawo mishi, sabida haka iya magana ba karamin gudumawa yake baiwa mutum a rayuwarshi ba".

"Sai Abu na hud'u wannan kuma sai an d'aura Aurenki kafin nafad'a miki, sabida su Amrah sun sake kunnuwa sunaji, yanzu kutashi muje kitchen akwai wasu kalolin abinci dazan koyar muku"

    "Idan tayi tsami ai Nima zanji ko?"
Cewar Amrah wacce taso ayi maganar gaba d'aya a gabanta,
Unty Sadiya tayi dariya tace "Ku tashi muje nikam muyi cake da coconut rice sai coconut juice"
Mikewa sukayi duka suka shige kitchen, Amrah da wayarta  ta shige kitchen d'in tana chatting nata, unty Sadiya ce tace "ba lokacin chatting bane yanzu lokacin aiki ne, mutum d'aya zan ragawa tad'au waya itace Fadila sabida Sweethert nata zai kirata maybe"
Amrah ganin komai sai ace Fadila yasa tace "dad'in abun ai nima macece kuma watarana zanyi saurayin"
Unty Sadiya cikin wasa tace "Ke ai banga samarai suna rububinki ba duk da kinfi Fadila kyau da class Amma ita hakurinta yasa tana samun maza kamar ruwan sama"
Maganar ta konawa Amrah rai jitayi bazata iya zama a kitchen d'in ba, fita tayi a fusace tana jin ranta yana kara b'aci.


_Jiddah Ce...
08144818849