Sanata Ibrahim Lamiɗo dake wakiltar yankin Sakkwato ta gabas a majalisar dattijai ta Nijeriya an fara raɗe-raɗi a Sakkwato zai bar jam'iyarsa ta APC zuwa sabuwar jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Mutane a jihar sun fara raɗe raɗin ne tun bayan da aka samar da haɗakar, da cimma matsaya kan tafiya ɗaya don ganin an kayar da APC a ƙasa.
Ganin yadda Sanatan ke da mu'amala mai kyau da 'yan adawa a jiha, bai shiga harkokin gwamnatin APC a Sakkwato, magoya bayansa daban na gwamnati daban hakan ya sa da yawan mutane musamman 'yan siyasa suka kai ga matsayar cewa da wuya siyasar 2027 Lamiɗo ya tsaya a APC, wannan na cikin abin da ya haifar da jita-jitar zai koma ADC kafin a gudanar da babban taron jam'iyar a kasa.
Ɗan siyasa kuma magoyi bayan APC, an sakaya sunansa ya ce suna zargin Sanata Ibrahim Lamiɗo zai bar jam'iyarsu tun kafin yanzu ganin yadda yake da tsamin hulɗa da jagoran APC Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu abin da ya kai ga ba a ganin su a wuri daya a kowane taro a jiha da wajen ta.
"Ba za mu yi mamakin Sanata Ibrahim Lamiɗo ya bar APC ba don ba mu tafiya a tare da shi, sama da shekara ɗaya duk wani taro da za a yi a gidan gwamnatin jiha ko a gidan Sanata Wamakko ba ka ganinsa hakan ya nuna mana ya tafi daban mu 'yan APC mun tafi daban," a cewarsa.
Kabiru Wurno ya ce maganar Sanata Lamiɗo zai iya komawa ADC abu ne da za a ce zai iya faruwa tun da shi ɗan siyasa ne kuma ita yake yi bai bari ba, da alama kuma yana son ya sake komawa kujerarsa a 2027, da wahalar gaske ya samu damar tsayawa a APC don baya tare da shugabanninta a matakin jiha na ƙasa da yake tare da su ba za su iya ba shi damar ba, ka ga dole ya yiwa kansa mafita, bana mamakin ya fice daga jam'iyar.
Shu'aibu Muhammad da ya fito a Sabon Birni ya ce shi baya son Sanata Lamiɗo ya bar APC don yanada muhimmaci a siyasar yankin Sakkwato ta gabas amma in zai fita ba zai hana shi ba.
"Na samu labari a gari ana ta yaɗawa cewa Sanata Lamiɗo zai koma ADC hakan zaɓinsa ne amma ba haka na so ba, da zai koma ya shirya da Sanata Wamakko zai fi don siyasar Gabas na buƙatarsa tare da su.
"In ka duba a tare suka nemi goyon baya a 2023 yakamata a cigaba da tafiya tare don nasarar APC, shi kaɗai ba zai iya ba, in ka yi duba shi sabo ne a fagen siyasa amma taimakon da yake yi, ya taimake shi sosai siyasarsa ta ɗaga zuwa wani mataki, amma ja da Wamakko lokacin da yake da mulki a hannu sai an shirya sosai kafin a yi nasara kansa.
"Sanata Lamiɗo zai bar gwamnati ya kuma je neman gwamnati kamaar ni naga yin haka wauta ce, wannan maganar da ake yawo da ita a jihar Sakkwato zai koma ADC naso ya sauya tunani kanta," a cewar Sabon Birni.
Ya'u Muhammad Goronyo ya ce ya ji labarin amma sun ɗauka jita jita ce don ba wata magana a hukumance daga Sanata Lamiɗo amma in ya yanke shawarar barin APC yana tare da shi.
"In Lamiɗo ya yanke shawarar barin APC muna tare da shi zuwa ADC don a ceto talaka a halin da ya shiga a jiha, nasan zai iya domin shi matashi ne da ke tare da matasa saboda halinsa na taimako musamman samar da aiki ga matasa da kula da matan da suka rasa mazaje a matslar tsaron Sakkwato ta gabas."
Wani na kusa ga Sanatan ya ce ba zai ce komai kan maganar ba, a tuntuɓi sanatan don shi yafi dacewa ya yi magana kan lamarin.
Sanata Lamiɗo waƙilinmu ya tuntuɓe shi a waya kan maganar da ake yi a Sakkwato shin da gaske ne zai bar APC zuwa ADC, sai dai bai kusa ga wayar, kuma an tura masa sakon kar ta kwana, Distinguish Sanata ana yada cewa za ka bar APC ka koma ADC, shi ne muke son jin ta bakinka, bai ce komai ba har lokacin hada rahoto.