NNPP ta rushe shugabancin jam’iyyar a Kano yayin da Gwamna Abba ke shirin sauya sheƙa

NNPP ta rushe shugabancin jam’iyyar a Kano yayin da Gwamna Abba ke shirin sauya sheƙa

Uwar  jam’iyyar NNPP ta ƙasa ta rushe dukkan shugabancin  jam’iyyar a Jihar Kano, daga matakin jiha har zuwa matakin karamar hukuma da na mazabu.

Sakataren yaɗa labarai na na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an ɗauki matakin ne bisa tanadin kundin tsarin jam’iyyar NNPP.

Johnson ya ƙara da cewa za a sanar da kwamitocin rikon ƙwarya da za su jagoranci harkokin jam’iyyar na wucin gadi nan ba da jimawa ba.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar rikici a cikin jam’iyyar, biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC. Wannan yunƙuri ya gamu da adawa mai ƙarfi daga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.