Ina Sana'ar Dambun  Kaza Don Dogaro Da Kai, Ba Don Kaskanci Ba------Hajaru Muhammad

Ina Sana'ar Dambun  Kaza Don Dogaro Da Kai, Ba Don Kaskanci Ba------Hajaru Muhammad

 

Daga Muhammad Nasir.

Hajaru Muhammad tana  zaune a jihar Sakkwato anan ne take gudanar da sana'arta ta sayar da Dambun Kaza, ta shahara a wurin tallata hajarta a kafofin sadarwar zamani, Managarciya ta tattauna da ita kan sana'arta da fatan da take da shi a gaba.

 

Amatsayinki na matashiya akwai mamaki ki reni sana'a har ta samu cigaba, mi ya baki kwarin guiwar shiga sana'ar karan kanta.

Abin da ya bani kwarin guiwa a gidanmu ana yin abubuwa da suka shafi kayan buki hakan ya sa na rungumi sana'ar dambun Kaza na rika yi don tashi a cikin sana'a.

 

Idan mutum yana son fara sana'ar Dambun Kaza ta yaya zai soma.

Da farko za ka samu kaji manya domin kanana ba su yi, sai ka wanke su ka gyara ka dafa su irin dafuwar Farfesu, ka sanya duk kayan da kake bukata a ciki har sai sun dafu sun watse da kansu kashi ya rabu da tsoka a cikin Tukunya. Daga nan ka sauke ka samo wata tasa, da za ka yi suya da ita a haka za ka rika zuba wannan tsokar ba da kashi ba, kana suya da kanta za ta watse ta yi dambu ba sai an daka shi ba, in kana so za ka iya dakawa ya danganta.

 

A san da kika fara sana'ar a yini kin samu cinikin kudi kimanin nawa, yanzu kuma da an ka sanki kuma fa.

A lokacin da na fara sana'ar a yini zan samu cinikin 3000 zuwa 4000, ina sayar da roba 500, ba na kula da riba a lokacin, a yanzu kuma na kan samu ko nawa daga dubu 10 ko 20 har sama da haka, roba nakan sayar da ita 2000 a yanzu.

 

Wadanne kalubale ne kike fuskanta a cikin sana'arki ta dambu.

Abin da na fi fuskanta bai fi yaudara ba, tun da a online nake kasuwancina, sai ka ga mutum ya ce na aika masa dambu na kaza a jihar da yake zaune bayan na aika, kudina a ki bani su daga uzurin network har na fahimci baya bayarwa ne, sai kuma in ina talla a turkata ko a kasan rubutun wani  a dinga zagina, hakan ba dadi.

 

Nasarorin da kika samu da ba zaki manta da su ba.

Gaskiya na samu nasarori da yawa kuma ina jin dadin haka, iyayena sun daina bani kudin sayen handout, kanena in zai je makaranta ni ke bashi kudin break, ina yi ma kaina lalurori da dama ina jin dadin haka.

 

Kin zamanantar da sana'arki sabanin yanda ake tallar sana'a a Sakkwato mi ya tasirantar da ke kika yi haka.

A gaskiya ina facebook hakan ya na yanke shawarar fara tallar dambuna a wurin, sai na ga mutane suna so kuma ina kara samun flowers kafin na fara tallar 1k nake da su amma yanzu ina da 41k ka ga da tasiri kenan ta sanadin sana'ar nan. Ina fatan sana'ar ta dore nafi haka har na samar da wata masana'anta ta yin dambu wadda take mallakina. A yanzu cikin sana'ar nakan a jiye wani abu don bunkasa sana'ata.

 

Sana'ar dambun nama nada sirri da ya bambanta ta da sauran sana'o'i?

Eh, tau yana da riba sosai har dai in ka inganta shi, gaskiya ina samu a sana'a ta, a cikin wadanda muka yi hulda a sana'anta wanda ba zan manta ba bai fi dan kwallon Nijeriya ba waton Abdullahi Shehu da ya turomin dubu 80 kawai don in bunkasa sana'ata, haka ma masayana suma suna raina.

 

Wane fata kike ga masayan dambunki.

Su yi hakuri dani musamman masu yi min magana a messenger, sha'anin hulda da wuya yake, ina sana'a ne ba don kaskanci ba sai don dogaro da kai, a daina kallon masu sana'a mata a matsayin wasu kaskantattu ba haka ba ne, neman na kai nada amfani.