Abin Da Babba Ya Hango:Fita Ta Bakwai
Sosai take cin duniyarta da tsinke , yanzu ba ta ma cika zama a Nigeria ba , idan ka ganta yanzu ba za ka taɓa gazgata ita ba ce, domin kuwa lokaci ɗaya duk ta canja.....
RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
Fita Ta Bakwai
Sosai hankalin Umma ya tashi lokacin daya zayyane mata abin da ya faru.
Kallonsa ta yi ta ce "ai da ba sakinta za ka yi ba, irin su kyanta a dinga ɗaurasu a kan hanya ko Allah zai sa su dawo hanyar da ta da ce, amman tunda harka zartar da hukuncin, Allah ya sa hakan shi ne ya fi alkheri ya haɗa ka da mace ta gari."
Da "Amin ya amsa", yana mai cigaba da dana sani a cikin ransa, gaba ɗaya wata irin kunyar Umma yake ji, jikinsa a sanyaye ya ce "Umma dan Allah ki yafemin wallahi Allah ni kaina ba zance ga dalilin daya sa na nace mata ba."
Ɗan murmusawa ta yi sannan ta ce "ni tun yaushe komai ya wuce a guna, ai dama *DUK ABINDA BABBA YA HANGO YARO KOYA HAU TSAUNI BAZAI GANSHI BA!*, tun lokacin da ka zomin da zancen yarinyar hankalina bai kwanta da ita ba, sai da nasa aka yi min bincike aka zomin da labari marar daɗin ji dangane da ita, amman naso na lurar da kai a lokacin ka ƙi, ka ga ai kanka kayiwa ba ni ba, na tabbata har abada ba za ka taɓa samun macen kirki irin wace naso ka aura ba, na jima banga yarinya wace take da hankali da nutsuwa da kamala irinta ba, amman dama haka Allah ya nufa ba matar ka ba ce daman, ni yanzu ba abin da ya dame ni sai dai na ce Allah ya sa hakan shi ya fi alkheri a gare ka da mu baki ɗayanmu, ya ba ka mace ta gari, don kasan ba za ka zauna min a haka ba mata ba, gaka ga su 'yan biyu gwanda na ji da su, su mata ne."
"Idan hankalinka ya kwanta nan da wata ɗaya sai ka fara neman matar aure don shi ne rufin asirin ka."
Sosai kalaman Umma suka shige sa, ba ma kamar maganar auren da ya ji ta sanyo tun yanzu, dan shi kam yana ga ba shi ba wani aure, tunda har matan haka suke ko wace muaradinta ta cutar da kai.
Ya jima a gurin sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa tun na samartaka.
Sosai su 'yan biyu su ka yi murnar jin labarin sakin da yayansu ya yi wa Zuly, sun yi murna har saida Umma ta dinga yi masu faɗan su daina ba kyau.
★★★★★★
Sosai suka ji jiki don kuwa ba ƙaramin duka ya yi masu ba, suna isa gidan Hajiya Turaia Parlour suka zube suna sauke numfashi, kiran Ruka Hajiya Turai ta yi ba da jimawa ba ta zo, zare idanuwa ta yi tana tambayarsu waya yi masu wannan ɗanyen aikin.
Ba wace ta bata amsa ,suka mika mata key ta jasu sai hospital, magunguna aka rubuto masu kana aka yi masu dresing ɗin mikin da suka samu.
Gida suka dawo anan Parlour suka dinga jinya har lokacin da suka samu sauƙi.
*Bayan wata biyu*
Zuwa wannan lokacin komai ya wuce a gurin Kasim ba abin da ya ke gabansa sai neman na kansa.
Umma kuwa ta sa masa idanuwa akan batun aure shi kuwa gaba ɗaya kansa ya kwance, don sh ikam wace zuciyarsa ke so yana jin kunyar tun kararta da zancen, ga shi Umma ta sanyo sa gaba kasan cewar saura wata ɗaya bikin su 'yan biyu don tana son a haɗa da nasa.
Yana kammala cin abinci ta kallesa sannan ta ce "naga kana yimin yawo da hankali fa a kan zancen da nake yi maka, to wallahi ka kiyaye ni".
Duƙar da kansa ƙasa ya yi sannan ya ce "Umma na samu wacce nake so fa, kawai na kasa tunkarar tane da maganar".
"To mi aka yi kenan?, ai da ita da babu duk ɗaya, gwanda ma ka je ka gaya mata yafi don nikam Allah na gaji da ganin ka haka, ace mutum kullum cikin azumi yake haba ka yiwa kanka Wa'azi mana,."
Ɗan sosa kansa ya yi sannan ya ce "tau Umma zan gwada na gani."
Da haka ya miƙe ya nufi ɗakinsa yana tunanin ta gunda zai ɓullowa lamarin.
Bayan ya dawo daga sallar isha'i ya harɗe cikin farar shadda kirar 'sky blue' sai tashin ƙamshi ya ke yi, kai tsaye cikin gidan ya nufa gurin ƙanen mahaifinsa wato mahaifi ga Maimunatu malam Shehu.
Bayan sun gaisa ne ya duƙar da kansa ƙasa kana ya hau koro masa bayani.
Sosai ya ji daɗin lamarin ko bakomai za a ƙara ƙarfafa zumunci.
Damar tuntuɓar ta ya ba shi don suji ta bakinta.
Cike da ƙwarin gwiwa kuwa ya nufi zauren gidan yana jiran Malam ya turo masa ita kamar yadda ya ce.
Tun daga shigarsa gidan ya kira ta ita da mahaiyarta Inna Kulu ya yi masu bayani.
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe ta lokacin da ta ji wai yazo neman ta.
Cike da murna kuwa ta ɗan gyara fuskarta ta fita zuwa gurin da yake.
Wace ce Maimunatu?.
'Ya ɗaya tilo a gurin Malam Shehu da Inna hauwah, yarinya ce 'yar shekaru 18 da haihuwa, baƙa ce amman ba irin bakinnan sosai ba, 'yar guntuwa da ita , yarinya mai hankali da nutsuwa uwa uba ilimin Islama dake cikin kanta.
Wannan kenan.
Tana fitowa ta tarar da shi anan gurin da ya nema ya yi tsaye, gaida shi ta yi sannan suka yi shuru su dukan su.
Sai bayan 'yan mintuna kana ya ɗago da kansa yana kallonta, cikin sanyin murya ya yi mata bayanin abinda ke tafe da shi.
Ba wani ɓata lokaci ta yi na'am kuwa don dama tana son abinta ba ta tsaya wani ja'inja ba ta amince.
Soyayya suke gudanar wa mai cike da tsafta da girmama juna.
Ba'a ɗauki tsawon lokaci kuwa aka sanya ranar aurensu lokaci ɗaya dana su 'yan biyu.
Lokacin biki sai ƙaratowa ya ke yi, shirye-shirye ake yi ako wane ɓangare barma Umma da za ta aurar da ƴara har uku.
Ya sayar da gidan da suka yi rayuwa da Zuly ya saye wani a kusa da su Umma, gida ne babba mai ɗauke da ɗakuna huɗu da babban Parlour, sai kitchin.
Sosai shi ma ta nasa ɓangaren yake shirye shiryen bikin idan ka ga yadda yake rawar ƙafa za ka yi zaton wannan ne auren sa na farko.
Yau ne suka gudanar da wanki amarya, sosai aka yi shagali na ban mamaki, amare sun yi kyau abinsu idan ka gansu kamar ka ɗauke su ka tsere sai fitar da annuri fuskansu ke yi.
Ranar juma'a aka ɗaura aure bayan kammala sallar juma'a, ɗaurin auren ya samu halartar mutane da yawan gaske.
Da daddare a kayi masu nasiha sosai kana daga bisani aka miƙa su a ɗakunan mazajen su.
Tau sai muce Allah ya bada zaman lafiya.
Zuly.
Sosai take cin duniyarta da tsinke , yanzu bata ma cika zama a Nigeria ba , idan ka ganta yanzu ba zaka taɓa gazgata ita ba ce, lokaci ɗaya ta canja.
Ko yanzu tafe suke ita da Alhaji Sambo da Hajiya Turai a cikin mota daworsu kenan daga Dubai yawon shakatawa, sun hau titi kenan wata babbar mota tabi takan motarsu, ko da a ka fito da su daga cikin motar Alh. Sambo rai ya yi halinsa ita ma Hajiya Turai ta rigamu gidan gaskiya Zuly kaɗai ce wace gaba ɗaya ƙafafuwan ta sun samu matsala.
Kai tsaye asibi aka kaita, dole sai da aka yanke dukkanin ƙafafuwan ta.
Sosai duniya ta juya mata baya, ba ta da komai face 'yar keken da take kai a kai ita ke tuƙa kanta duk inda za ta je.
Rabbu yasa muyi kyakkyawan ƙarshe.
Amarci ake ci ba kama hannun yaro, sun yi kyau sun yi haske sosai, suna ci gaba da rainon ɗan ƙaramin cikin dake jikinta.
Tau Rabbu ya raba lafiya.
TAMMAT BI HAMDALLAH.
Duka duka anan nakawo ƙarshen wannan ɗan taƙaitaccen labarin ina roƙon Ubangiji Allah yasa abinda na rubuta al'umma su yi aiki da shi wanda ba shi da kyau marar amfani kuwa Ubangiji Allah ya sa a yi watsi da shi.
Kura kurrain da na rubuta Ubangiji Allah Ya yafemin.
Kuyi haƙuri da yadda labarin ya zo a ɗan kadan ba laifina ba ne lokaci ne bai bani damar hakan ba, ku ci gaba da bibiyata ako'ina.
08136402046
Mu Hadu a Wani Littafi na Daban.
Maryamah