WANI GIDA: Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta Biyu
WANI GIDA
*(GIDAN GADO)*
*RUBUTAWA DA TSARAWA*
*ZAINAB MUHAMMAD*
*(Indian Girll)*
*Alƙalami Writers Association*
*A.W.A*
*{Alƙalami yafi takobi Alƙalaminmu ƴancinmu,Rubutunmu basirarmu,Rubutu danci gaban al-umma}*
*Wannan littafi na Kud'ine akan 200 kacal ta hanyar turo katin mtn ta wannan number 07063452697*
*Shaidar biya ta wannan number ayi WhatsApp: 09025892708*
*BIS-MILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*2&3*
********
Nufaisat ce zaune akan tabarma a tsakar gidan tana cin abinci hannunta ɗauke da note book ɗinta na makaranta da alama karatu take,Ihsan(ƴar autar su Nufaisat ce) ce ta zauna kusa da ita tare da fusge littafin ta gudu wajan Mama dake zaune a ɗaki tana sallah.
Miƙewa Nufaisat tayi ta bita ganinta jikin Mama bai hanata daketa ba sannan ta kwace book ɗinta ta fice,kuka Ihsan ta saka tana burgima.
Mama data idar da sallah ta fito ta sami Nufaisat aikwa ta rufeta da faɗa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.
"Tsabar rashin mutuncin ki biyo ƴar har gabana ki dake ta,to wallahi idan baki wasa ba saina saɓa maki shashasha!"
Dagowa Nufaisat tayi tana kallon Mama har ta gama maganar,miƙewa tayi cikin fushi ta a jiye abincin tai ɗaki sai kuma tasa kuka.
Haka taita kukanta Mama kuwa ko kallonta bata yi ba,sai da lokacin tafiya makarantar magriba ya yine ƙawarta ta biyo mata sannan ne Mama ta shiga ɗakin,kwance ta sami Nufaisat ɗin akan gado idanunta a rufe kamar mai bacci amma Maman ita ta san ba baccin take ba.
"To ki tashi ki fita ga Rahma can ta biyo miki makaranta"
Cikin dashashshiyar murya tace"Ba zani ba"
Mama ta dubeta kafin,Tace"Me kika ce"
"Ba zani ba kaina kemin ciwo"
Nufaisat ta faɗa lokacin da hawaye suka gangaro daga fuskarta.
Mama ta kau da kai gefe,sannan Tace"To wane ya sa maki ciwon kan,kinga ki tashi ki fito tana jiranki"
Tana faɗar haka ta fice daga ɗakin.
Miƴewa Nufaisat tayi riƙe da kanta saboda kukan da ta sha ta ɗauki hijab ɗinta ta fito,ko sai mun dawo ba tace da Mama ba ta bi bayan Rahma suka fice.
A hanya bata ce da Rahma komai ba har suka isa makarantar.
Suna zuwa suka gaida malamai sannan suka shiga aji.
Saida aka kusa tashi sannan wani yaro ya shiga ajin su Nasreen yace wai tazo inji malam jabeer.
Sai da tai kamar ba zata ba,sai kuma ta tashi ta fita,a can inda malamai suke zama idan ba aji zasu shiga ba ta same shi akan tabarma.
Sallama tai sannan ta zauna tare da gaishe shi,ɗagowa ya yi ya kalleta ya ga fuskar nan a ɗaure.
"Nufaisat me akai maki kika zo yau ba fara'a alhalin keda idan kika zo sai kowa yasan sa zuwanki?"
Malam Jabeer ya tambayeta.
Kanta a ƙasa Tace"Malam ba komai"
Malam Jabeer ya sake Cewa"To amma yau me ya sa bako ɗuriyarki ba a ji?"
Ta kalle shi sannan ta ɗauke kai,da Cewa"Kaina ne yake ciwo shiya sa"
Malam Jabeer Yace"To shikenan Allah ya sauwaƙe,ta shi ki koma aji naji ana addu'a"
Miƙƙewa tayi ta koma aji akai musu sallama aka tashe su.
Gidan su Maryam ne a farko dan haka ta riga Nufaisat shiga gidan.
Da sallama Nufaisat ta shiga gidan su,Mama dake zaune kan tabarma ta amsa.
Ɗaki Nufaisat ta shige ta aje hijab da jakarta sannan ta fito falo tai shimfiɗa ta kwanta.
*Washe gari*
Da sassafe Nufaisat ta tashi daga bacci dan ranar za su fara zana jarrabawarsu ta Neco(wato jarrabawar fita daga secondry,bayan ta gama shiryawa ne Mama ta bata ɗari tace ta sayi akwara taci kafin su dawo.
Haka suka tafi makarantar jarrabawar ba tayi wata wahala ba dan da nan suka gama suka dawo gida.
managarciya