A fara duban watan sabuwar shekara a gobe Jumu'a-----Sarkin musulmi

A fara duban watan sabuwar shekara a gobe Jumu'a-----Sarkin musulmi

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya umarci al'umma da su soma duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1446 daga gobe Jumu'a 5 ga Juli 2024.
Amadadin Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a masarautar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaid ya fitar da sanarwar.
Farfesa ya ce duk wanda ya samu ganin watan ya sanar da majalisar Sarkin Musulmi ko wani uban kasa ko hakimi domin sanar da al'umma.
Watan Muharram shi ne watan farko a tsarin watanni 12 na  shekarar musulunci.