HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
*Happy 5 years anniversary Kainuwa
Page 27
Barista Alawiyya ce dubi Daddy da Dr. Faisal tace, "Kuma an ja maku kunne ne? Anyi maku albashir da ajalinku idan baku saka baki na janye daga niyyyata ba halan?"
Daddy ne ya fara bata amsa, "Ta ya kika san me aka gayamin haka Alawiyya? Tabbas sun ce min ko dai nasa ki janye ko kuma na rasa raina na rasa ki baki ɗaya kuma tabbas Fatima sai ta mutu."
Kallon Dr. Faisal tayi ba tare da tace komai ba, amma shi da yake yasan halin ƴan kayansa sai ya bata labarin abin da take son ji kawai.
"Sun tabbatar min da cewa zan rasa ki kamar yadda zan rasa yarana tare da Ni kaina a banza idan ban sa kin janye daga shari'ar nan ba."
Fatima ta sake fashewa da kuka tace, "Kinga abin da nake gaya maki ko? Tabbas ba za su bar ku ba, basu da imani sun yi ƙaurin suna wajen tarwatsa rayuwar mutanen da basu ji ba, haka basu gani ba, don haka don Allah ku yi haƙuri ku manta da Ni tunda daman mun manta da Ni ku saka a ranku cewar ban duniyar baki ɗaya daman, don Allah ku yi min alfarmar barina a nan ku je."
"Wallahi ba zai yiyu ba, sam hakan ba zai faru ba ko a mafarki ba zan iya juya maki baya ba Fatima balle a ido biyu, kin san iyakar shekarun da na ɗauka ina jiran wannan damar ta sake ganinki? Shi ne don na cika marar rabo wanda bai san darajar soyayya ba sai na ƙyale ki? To tabbas ki saka a ranki idan mutuwa za ki yi to tare da Ni za ki mutu Fatima." Cewar Daddy kenan yana zubar da hawaye.
"Tabbas ka cika miji na gari abin koyi ga dukkan maza, ina bayanka nima zan bi dare, rana, don tabbatar da cewa mahaifiyata tana cikin natsuwa ta manta komai ta koma cikin farin ciki na wanke ta daga duk wani baƙin fenti da akai mata a idon duniya, nasa duniya ta karramata ta bata KAMBUN YABO."
"Ashsha! Anya kuwa kin san su waye Hajiya Turai da Hajiya Tani ƴar nan?"
To su ɗin manyan tantirai ne masu taƙama da kuɗi da tsafi."
A Yau bari na baku labarin asalin abin da ke faruwa ko kun yadda da maganata, ku yi ma kanku karatun ta natsu ku cire hannu daga lamarina, saboda na riga na shiga tarkon matan zamani masu gadara da kuɗi masu taƙama da shirka waɗanda basu ɗauki aikata zunubi wani abin tur ba.
LABARIN FATIMA
"Lokacin da Bello ya zo neman aurena, ban amince ba, saboda ban son nayi nesa da yarinyata da Inna, saboda nasan duk duniya su kaɗaine dangina ahalina kuma, sannan har ga Allah ina tare da son mijina Baban Alawiyya duk da ina ji a jikina danginsa ba zasu taɓa amincewa ya aure Ni ba haka ba zasu yadda da amsar Alawiyya ba matsayin jininsu ba yasa na yanke shawarar zama ba aure na fi amincema na zame ma Alawiyya Uwa kuma Uba ban san a wayi gari tai kukan rashin Uba don haka na ƙi amincewa da maganar aure ga duk wanda zai zo guna da sunan neman aurena.
Sai dai zuwan Aliyu yasa mutane fara gulmace-gulmace ana cewa na aje soja cikin gidanmu na ƙi aure, wasu marassa tsoron Allah ma suka fara cewa ita ma Alawiyya a haka na same ta, wannan maganganun ne suka saka Inna tai min magana kan na yi haƙuri na fitar da wanda nake so kawai yafi mutunci kuma hakan zai dakushe wancan baƙin suna da ake son dinga kiranki da shi na marar Uba.
Hakan yasa na amince da Aliyu domin ya yi min alƙawarin zai aje nan nan garin ba inda zai kai ni, ya tabbatar min da cewa bai da kowa sai Ni, don haka na ji na amince da shi domin ban san na sake yin na aurena da Babanki , rana guda danginsa suka zo suka rabamu har ma suka ƙi ɗaukar ɗiyarsa suka ce basu ɗauke ta matsayin danginsu.
Cikin lokaci kaɗan akai aurena da Aliyu Soja ya kama mana haya a Tabkin fili muka tare, ya ce na tafi da yarinyata amma nace a'a saboda har ga Allah ban san ɗiyata tai agolanci wani gida nasan Babanta ba zai murna da hakan ba.
Cikin ikon Allah Aliyu na kulawa da Ni yadda ya kamata, sai dai har zuwa lokacin ina danne zuciyata ne kawai amma Babanki ya ƙi barin zuciyata.
Kwatsam! Bayan wata shida da aurenmu wata rana Aliyu ya fita ya dawo da alamar damuwa, nai tambayar duniyar nan amma sai ya ce min ba komai kawai. A haka muka tafi da shi har kwana uku sai a na huɗu ne ya kira ni bayan ya dawo da rana, ya dube ni ya ce, "Fatima don Allah ki yi haƙuri ki yafe min duk abin da ya faru, wallahi ba laifina bane ba, na riga nayi bincike sosai kanki na fahimci cewar idan na gaya maki gaskiyar koni wanene to ba za ki aure ni ba, Ni kuma har ga Allah kece irin macen da nake mafarkin aure, hakan yasa nayi maki ƙaryar cewa Ni ɗan nan garin ne amma ba haka bane ba, Ni ɗan asalin garin Kaduna ne a unguwar tabkin Malamai nake zaune sannan Ni ɗin babba ne a cikin aikina domin saura shekara biyu nayi ritaya, ina da matan aure biyu Hajiya Turai da Hajiya Tani, duk a gidana suka je Makkah insha Allah ke ma zan biya maki sai mu je tare daman ina son na sake zuwa. Shekaru da dama nayi aure amma Allah bai taɓa ban haihuwa ba na nema har na gaji na fawwala Allah lamarinsa nasan dai shi ne mai badawa haka kuma shi ne mai hanawa.
Don Allah ki yi min alfarma ki yi haƙuri ki bini Kaduna na amince ki tafi da Inna da Alawiyya tunda dama na gaya maki ban taɓa haihuwa ba Ni kinga sai Alawiyya ta ɗebe min kewar yara a gidana don Allah Fatima."
Jikina baki ɗaya ya yi sanyi, tabbas da ya gaya min cewar yana da mata kuma yana da tarin dukiya ba zan aure shi ba, gwara na auri daidai Ni talaka, ina Ni ina zama cikin manyan Hajiyoyi?"
"Fatima don Allah karda ki tada hankalinki kan wannan maganar wallahi na rantse da Allah zan kula da ke yadda ya kamata ba zan taɓa barinki ki yi kuka ba a rayuwarki insha Allah ki ban amanarki zan riƙe maki ita da hannu biyu insha Allah."
Ya zan yi? Aure ya wuce komai sannan ya wuce ai wasa da shi don haka na shirya na je na gayama Inna komai. Ita ma jikinta ya yi sanyi kan lamarin amma haka tai ta ban ƙwarin gwiwa, haka na sake bata amanarki na taho cike da tashin hankali lokacin kina makaranta haka na je ta can na tsaya ina hangen ki ke da ƙawarki Jiddah ɗiyar Iyami mai abinci. Ba ƙaramin kuka nayi ba da zamu tafi amma haka na dangana muka tafi ta kan jirgi, duk da cewar Ni ma asalina ba matsiyaciya bace haka nake Makkah sai da na zama kamar wata ƴar ƙauye saboda an kwana biyu ba a gamu ba.
Lokacin da muka sauka filin jirgin Kaduna, nayi mamakin manyan motocin da suka zo tarbar mu,kai tsaye wani babban gida muka nufa wanda ya tuna mun asalin gidanmu da ƙasarmu, har hawaye suka zubo min, na share ina hasko fuskar iyayena da Yayyena.
Sashe uku ne cikin gidan, kai tsaye duk inda ya taka ƙafarsa nan nake aje tawa, cikin wani babban falo naga mun shiga ga ƴan aiki nan cike da gun sai kai kawowa suke, kujera ya nuna min na zauna cikin natsuwa da fargaba cike da zuciyata, damuwa shimfiɗe a kan fuskata.
Nan da nan aka cika min gabana da kayan ciye-ciye, Ni dai kaina ƙasa na kasa ko ɗaga kaina balle na samu sukunin cin abin da ke gabana.
Ya jima zuwa can sai naga ya fito ta wata ƙofa wadda ba ta ita ce ya shiga ba, bai jima da fitowa ba ya zauna sai ga wata dakekiyar mata ta fito ta wata ƙofa ta ci uwar kwalliya sai taunar cingam take tana hura hanci, ko ban tambaya ba nasan cewa ranta a ɓace yake yadda ta watsa min wani mummunan kallo ta hakimce kan kujera ta turo kallabinta gaban goshi. Ina cikin satar kallonta ne wata ƙofar ta buɗe sai ga wata Hajiyar ita ma, ba ƙarya ta ci kwalliya sosai kamar ta so tafi ta farkonma.
Su duka suka tsare ni da idanu wanda ba alamar fara'a a kan fuskarsu.
Maigidan ne ya fara magana bayan ya yi gyaran murya.
"Alhamdulillah! Na ji daɗi da na dawo na iske ku lafiya kamar yadda na barku lafiya. To cikin ikon Allah kamar yadda ba kira kowace daga cikinku na gaya mata zan ƙara aure kafin na ƙara ɗin, da na ƙara kuma na kira kowacce na gaya mata na ƙara aure, to Yau ga matar da na auro daga Lagos mai suna Fatima...
"Ahayye warrr."
Abin da suka haɗa baki suka ambata kenan.
"To wallahi bari ka ji Alh. Baka isa ba ka kwaso mana rainon Lagos,zaman ƙasan gada ba a cikin gidanmu ba." Cewar wadda ta fara shigowa kenan.
"Ai Hajiya ke kika tanka ma har aka ji ta bakinki, Ni kam ai sai dai a gani a aikace." Cewar wadda ta zo daga baya kenan.
Ya girgiza kai ya ce, "Ban san abin da kuke gaskiya, ya kamata ace kun ƙara hankali kan wanda gare ku, saboda ku ba yara bane ba, na gaji da yadda kullum gidan nan ba zaman lafiya, sai kace na haɗa musulma da kafura haba!
"Warrrrr!
Ahayyye Warrr."
Tare suka sake haɗa baki gun furta kalmar Warrrr kamar wasu zararru.
Kallona ya yi, "Fatima waccan ita ce Hajiya Turai, ita ce ta fara shigowa sai wannan ita ce Hajiya Tani, su ne matana da na gaya maki guda biyu, Allah bai bamu haihuwa ba, har zuwa yanzu muna saka rai dai."
Ya nuna min wata ƙofa waccan ita ce hanyar sashen ki, nan ne ɓangarenki, ina son Allah kada ki biye masu ki ci-gaba da nuna min kyawawan halayenki masu kyau don Allah hakan zai sa na rage damuwar wasu abubuwan ban san rigima ban san tashin hankali ko da wasa."
Yana gama maganar ya miƙe tsaye ya nufi wata ƙofar ya bar mu a zaune a gun, su kam kowacce sai cika take tana batsewa.
Hajiya Turai ta kalli Hajiya Tani ta kwashe da dariya tace, "Hajiya wannan fa ita ce kishiyarki, don haka sai ki tashi tsaye Ni kam yanzu na aje makamai na kan wani banzan kishi sai na abin duniya, don haka Allah Ya bada sa'a Yasa a fara zuba ruwan kishi da kyau cikin lokaci kuma, domin irin waɗannan masu siffar munafukan Larabawan Makkah basu jin kira balle aiken dare sai kin tashi tsaye kin yi kamar kina yi sannan za ki samu galaba kan su."
Hajiya Tani ta maka min harara tace, "Ni wallahi kyanta ma ke ban tsoro, munafukar kamar haihuwar indiya ta tsakiya kin san ance sun fi kyau, ko a cikin indiyawan. Amma maganarki na kan hanya wallahi ba zan kwance ba daga kuka sai gari ba tai min yanka baya ba, kin san ance ƴan Lagos Mayun gaske ne idan suka kama kurwar namiji sai sun kai shi kushewa suke samun sa'ida a ransu."
Ni dai tamkar an dasa ni haka nake zaune ina sauraren su ina kuma ƙare masu kallo don tabbatar da cewa daga bakunansu maganganun ke fitowa ko ko ya akai ?
Hajiya Turai ta zabga min harara tace, "Naji Alh na kiranki da Hajiya shi ya biya maki kuɗin Makkah ko?"
Murmushi nayi domin ta tuno min da cewa nima naje Makkah tun ina budurwa ma.
Sai dai bakina ya yi nauyin da ban iya bata amsar tambayar ta.
Ganin ban da lokacin zama ina sauraren baƙaƙen maganganun da suke gaya min masu kama da barazana yasa na tashi na nufi ƙofar da aka tabbatar min da nan ne ɓangarena.
Sai dai tare muka tashi da su, ban ankara ba naga sun sha gabana, kafin nace me sun rufe Ni da duka.
Sai da suka gaji sannan suka ƙyale Ni, da jan jiki na shige ɓangarena ina hawaye.
Dare nayi aka aiko na fita cin abinci, kamar ince na ƙoshi sai kuma naga rashin dacewar hakan tunda Alh ne da kanshi ya aiko kirana.
Na ƙara gyara jikina don kar a raina Ni tunda naga matan gidan gasar kwalliya suke na fice ina duk addu'ar da ta zo bakina.
Su duka suka zubomin ido kowacce fuska ɗauke da tsana da kishi.
Da sallamata na isa gun, kamar yadda na zata hakan ya faru, Alh ne kawai ya amsa sallamar da nayi.
Shi na fara gaidawa sannan na bisu duka na gaida, amma babu wadda ta amsa min, shi ne kawai ya amsa gaisuwata yana ta murmushi.
Kular gabana na jawo na buɗe, ƙamshin abincin ya daki hancina sai kawai na ji cikina baki ɗaya ya shiga hautsinawa, kafin kace me, amai ya wanke jikina.
Su duka suka ɗora hannu a kai suka furta, "Kambura'uban can kayyasa! Ba dai ciki ne da ke ba?"
Mu haɗu a page na gaba don jin koma miye gare ta.
Taku a kullum Haupha!!!