ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 11
ANA BARIN HALAL...:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 11
Lokacin da na shiga ɗakin ummie na nasamu tana waya ne, a hankali na fahimci da mummyn su Aliyu take wayan, zuciya nane naji ya yanke, kasa kunnena nayi ina sauraran abun da suke faɗa, haƙuri kawai ummie ke ta bawa mummy akan ta kwantar da hankalinta komai nufine na Allah, Allah yayi babu aure tsakanin shi da Ayshaa, rabon da habiba ne, da yake ya wanci ummie idan zata amsa wayanta handsfree ta ke bari, sai idan na sirri ne sosai ba zata saka ba, tsaki mummy ta ja mai ɗan tsayi sannan tace, "wallahi ummin su rai na baya son haɗa iri da matar nan, don babu Allah a zuciyarta, amma bbu komai abunda ta keso bazata samu ba, don insha Allahu bazan bar ɗana a mallake ba, a farko kan sunyi nasaran chafko shi amma gaba kan tayi kuka da kanta", murmushi kawai ummie tayi sannan ta chanja zancen da wani chan daban, a haka kuma basu daɗe ba suka yi sallama.
Daga nan ummie ta juyo tana kallona fuskanta ɗauke da murmushi, ni kuma da sauri na ƙarasa wurin ta, gaisheta nayi, ita kuma ta tambayeni fatan babu wani matsala ko? Murmushi nayi na kwanta a kafaɗan ta, bance mata komai ba nayi shiru kawai ina kwance ido na a rufe, nasiha da kwantar da hankali na ummi tayi ta mun, tunin naji zuciyata tayi sanyi, muna a haka wayan ta ya fara neman a gajin a ɗauke shi, hannu ta saka ta ɗauka sannan ta saka shi a handsfree, muryan yayah mohd naji yana gaisheta, ni kuma na ƙara gyara kwanciyata a jikinta, kawai sai naji yayah na gaya mata Aunty bintu ta haihu, da sauri na miƙe zaune ina fara'a idona akan ummie nah da duk fuskan ta ya gauraye da murmushi, "ta samu boy, daga ita har babyn duk suna lafiya, muna asibitin", ya faɗa ummie kuwa sai fara'a ta ketayi, "insha Allahu mamanku suna zuwa yanzu, Allah ya raya baby da imani, ita kuma Allah ya bata lafiya da lafiyan shayarwa, suna ajiye wayan na rungume ummie ina "ummie munyi ɗa, wayyo ummi nayi ɗa," da sauri na miƙe nace "ummie bari na shiga wanka na bi mamah muje muga baby", ko jiran me zatace banyi ba na wuce toilet da gudu na.
Kafin kace me duk gidan mu ya kachame da murnan haihuwan barin ma hafsy da ta ringa tsalle kamar ƴar 6yrs, haka muka shiryah sai *NI'IMA HOSPITAL* mukaje mukaga yaro fari kyakkyawa, kana ganinshi kaga jinin gidan mu, sak Yaya mohd kaman wanda yayi kaki, haka muka ringa murna muna ta ɗaukan babyn, bayan 1hr aka sallame su, lokacin Aunty Rakiya ta iso ita da hajiya umma, mu kuma dama da mamah mukazo da hafsy sai driver, abun mamaki har muka gama murnan haihuwan nan babu mamie babu ƴaƴanta ko ɗaya, kuma duk suna gida, ganin zuwan su ummah nayi tunanin ita mamin zata biyosu amma shiru, haka muka ɗunguma gidan zuwa gidan yayan mu.
Muna zuwa muka samu Fatima ta gama gyaran gidan ko ina sai ƙamshin turaren wuta yakeyi, dama ana haihuwan yayah mohd yace ta koma gida ta gyara, amma bata ɗaura abinci ba daga gida ummin mu ta sa akayi, ana zuwa mamah ta saka ruwa ta wanke baby tsaff, Aunty Bintu kuma Aunty Rakiya ta shiga ta gasa mata jiki ta fito ta barta ta ƙarasa wanka.
Bayan kwana 2 sai ga yar maman Aunty Bintu ta taho daga maiduguri, dama mamah tun ran haihuwar muke gidan tare, sai ranan ta tafi, amma ni ina nan tare da fatima, ummie tace na zauna na taimakawa fatima.
Ranan suna yaro yaci sunan Abban mu wato *USMAN* amma sun mishi laƙani da *AREEFH* sai wajen dab da magrin sai ga mamie da su habiba driver ya kawo su, muna zaune a parlor nida su maryam da fatima, da wata ƴar'uwar su da suka zo suna mai suna Ayshe itama, muna zaune suka shigo, muna haɗa ido da mamie ta zabga mun hararah, ganin haka na ɗauke kaina a kan su, ganin akwai su maryam a wurin habiba ta tsaya, ita kuma raliya suka shige ciki ita da mamie, banyi niyyan kulata ba duba da ganin bata kula ni, duk da dai ni yau sati na guda da barin gida, ita kuma ba zuwa barka ma sukayi ba, kawai kaman daga sama naji muryan ta tana faɗin "sisto sabon waya kikayi ne"? Ɗago kai nayi ina duban ta fuska na ɗauke da murmushi na amsa mata da "ae yayi 2weeks ae, ranan da aka kawo ina gaya miki naga kin wuce kitchen da sauri, so nayi tunanin idan kin fito zaki zo ki gani ae", da sauri ta saka hannu ta karɓa tana juya shi, cike da mamaki tace, "kin san irin shi ne a hannun Baby", ta sake juya wayan a hannunta tace " Gaskiya wayan ta tafi da ni don tun ranan dana gani a hannun shi wayar ta mun, shi kuma yana cewa ta fi ƙarfi na, gashi kuwa a hannun sisto, aeko zan ce mishi batafi ƙarfi na ba, tunda sisto na ma shi ta ke riƙewa",
"chaɓ aiko tafi ƙarfinki, amma ta wani wuri kuma bata fi ƙarfin kiba, tunda naga alama ke duk abunda siston naki tayi sai kin nemi ƙwace shi zuwa gareki, kin ƙwace saurayi yanzu kuma kina shirin na waya, wai ke habiba baki ƙoƙarin yin abun kanki ne sai na wani? Inaga Babyn ma wanda kikayi ƙwacen ne kika mayar da shi Babyn ko?" cewar Fatima wanda ita dama kullum dare zamu kwanta ta dinga mitan wannan al"amarin, zuwan Ayshe ma jiya-jiya sai da ta bata labari, da yake dukkan su ƴan zafin kaine ita da ayshen sai abun su ya ɗauki zafi, ni dai da sauri na juya ina duban fatima da tayi maganan tana wani chin magani kaman zata kai duka, tana wani hararan habiba, miƙo mun wayan habiba tayi fuskan ta ɗauke da murmushi tana kallo na, bata tanka abun da fatima ta faɗa ba, sai ce mun tayi bari taje taga babyn sai ta dawo, hannu na miƙa na karɓi wayan da ta miƙo mun, tana barin wajen maryam taja wani dogon tsaki mtssssss, "yarinyar nan kullum na ganta kashe ni ta keyi da mamaki, kana ganinta kaman ta gari ashe zuciyar ta babu kyau ko kaɗan? Amma ba laifinta bane wlh, duk laifinki ne besty", maryam ta faɗa tana maida hararanta kaina, "good kin faɗi abun da yake zuciyata tun jiya, wlh tun jiya da fatima ta bani labari na kalli Ayshaa naga kaman bata wani damu ba sai kare ƴar'uwarta ta keyi, nace gaskiya Ayshaa itace mai laifin, don sai bango ya tsage kadangare yake samun ƙofa, idan ba sakacin Ayshaa yayi yawa ba ta yayah ƴar'uwata zata mun ƙwace a ƙaramin lokaci, haba jama'a wannan ma ae raini ne da chin fuska, sannan kuma babu daɗewa nazo ina buɗe miki baki ina miki dariya har ina miƙa miki waya na"? Aysha ta faɗa haushina cike da zuciyar ta, nidai bance komai ba banda mirmushin da nakeyi kaina a sunkuye ina kallon waya na kaman zan ga wani abu a ciki, amma zuciyata cike ta ke da damuwan maganan da habiba tayi, wato Aliyun ne ake ce mishi Baby? bayan haka ma yaushe yake zuwa gidan mu hiran da har taga wayan shi? Ikon Allah yanzu ya tabbata da gaske habiba tana son wanda ya so ni har yaso aure na?
Muryan Fatima ne ya dawo da ni kan tunani na danaji tana cewa, wai ko yanzu habiba ta kuskura ta dawo sai ta ƙara watseta, jin haka nayi saurin ɗago kaina nace mata "a'a fatima idan ummie taji raina zai ɓaci, don taja kunne na sosai akan maganan kuma tace bata son wani magana daga gare ni ya fito, don Allah ku bar maganan don ni yanzu ma duk kunsa naji babu daɗi, don gani zatayi kaman na damu ne yasa na gaya muku, don Allah kubari".
"dole ae kowa ya bari, tunda me abun bata so, mu ƴan abi yarima a sha kiɗa kuma mai ya talo mana? Allah ya bada sa'a", cewar maryam.
Babu daɗewa aka fara ƙiran sallan magrib, daidai nan habiba tazo inda muke, still fuskanta ɗauke da murmushi, gefe na ta zauna tana sake karɓan wayan hannu na, ban ja ba na miƙa mata, ƙasa-ƙasa take tambaya na waya saya mum? Murmushi nayi ina kallon inda ta buɗe, gallery nane wanda babu pic kowa sai na hafsy, sai kuma wannan babyn da aka haifa, sai kuma dukkan mu har da yayah mohd da babyn da maman babyn da mukayi yau da safe, bance mata waya saya mun ba sai murmushin da nayi, dai-dai wani photon da nayi riƙe da babyn a hannu na, lokacin na karkato da fuskan shi ya fito sosai, ƙurawa yaron tayi ido tana murmushi, chan ta ce, "sisto yaron nan kaman ke kika haife shi, kunyi kama sosai, Allah ya baki miji fari ku haifi irin wannan" ta faɗa tana ƙara zooming pic ɗin, nidai ban bata amsa ba sai murmushin kawai da na faɗaɗa shi, idon hafsy kaman zai faɗo ƙasa tsabar hararan da ta ke jefo mun, bai isheta ba ta ƙaraso inda muke ta miƙa hannu ta karɓi wayan a hannun habiba tana cewa, " Adda zamuyi photo da ƙawata" ko jiran amsa na batayi ba ta juya da wayan tayi ɗakin Aunty Bintu, nidai duk sai naji kunyan habiba, gashi su maryam sun wani nuna kaman ma basu san da ita a wurin ba, bai ishe su ba Ayshee tace su tashi suje suyi sallah suyi addu'a Allah ya rabasu da zuciyar cin amana, fatima kuma tana ƙarawa da kuma zuciyar son zuciya da ƙyashi da hassada, ita dai habiba bata ko kalle su ba idon ta kawai yana kan waya na, har sai da hafsy ma tazo tayi nata iskancin tukun ta ɗago idon ta danaga alaman kaman da hawaye, amma fuskan ta cike da murmushi ta dube ni, lokacin kuma mamie da raliya suka fito daga ɗakin mai jego, idon mamie akan mu amma kasan cewar Aunty bintu na bayan ta bata iya cewa komai ba sai harara da ta watsa mun, ƙasa-ƙasa tana hararan habiba, "tashi mutafi Addah, ko kuma sai an ɗaga ki amaryar Ali"? Raliya ta faɗa babu ko kunya a idon ta, tashi mukayi dukkan mu nida habiba muka tsaya, wani kallo mamie ta bini da shi na ƙasƙanci, a gadaran ce tace "ke kuma kin yafe school ne kika tattaro nan kika zauna? Ko aure za'a cire ki a miki tunda karatun yana takuraki?" ta faɗa tana mun wani banzan kallo, "mamie ae sai da white blood ake auren ko? Ae kawai kiyi shiru mamie mu wuce" raliya ta faɗa tana wani dariyan iya shege, daga ni har habiban kallo muka bita da shi, ganin haka Aunty Bintu ta dubeni tace, "Ayshaa maza jeki ɗakin yayan ku ki feshe shi da shelktox, ki rufe duka windows ɗin plz" ganin na samu sauƙin cin zarafin su akaina nayi sauri na amsa da tou na wuce ciki, bayan na amsa da tou, sannan nayiwa su mamie sallama, wanda ina gani bata amsa ba sai bina da harara da tayi
Washe gari na shiryah tun da safe na musu sallama na wuce gida sbd monday zan koma sch, duk da an koma tun last week.
Ranan saturday da safe wurin 11:00am na fito da coolern da ummie ta sakawa yayah Ahmad masan da tayi tun safe na kai mishi side ɗin su, a cikin kwando na haɗa komai na wuce side ɗin su, ina fitowa naga wata arnen mota ja a ƙofan su, a zuciyata nace ɗan gayun gidan mu ya chanja mota ne? Yaushe naji ummie na mishi faɗan yawan chanja mota da yakeyi, ina ƙara matsowa varander sai naga takalma kusan kala uku, a zuciya na nace tou hala ba motan shi bane, sallama nayi a bakin ƙofan, sau biyu nayi tukun aka amsa mun, yayah Ahmad ne ya amsa mun sannan ya bani izinin shigowa, buɗe ƙofan nayi na shigo ina ƙara wani sallaman, ban ƙarasa ƙarshe ba na yanke sallaman ya koma ciki, ido na ɗan zaro kaɗan...sai kuma nayi saurin maida nutsuwan jikina dai-dai, ganin ina shirin sake abun hannu na, "*AUNTY NICE* kin san suwa nagani a zaune?" kallonta nayi fuskana ɗauke da murmushi nace "a'a sai kin gaya mun hajjaju",
Wani fari da ido tayi fuskan ta ɗauke da murmushi da wani yangan ta da take burgeni da shi, "Fararen nan nagani zaune a parlon".
*AUNTY NICE*
managarciya