Ɗanyar Guba: Cigaban 3--4

Kai! Kamar matar Salis ce fa.' zuciyarsa ta tsegumta masa, ya so ya yarda da hakan sai ya samu kansa da tuhumar kansa. "Me zai kawo matar Salis a nan, kuma tare da wani saurayi?' ya jefa wa kansa tambayar. 'Amma fa kamar tasu har ta ɓaci idan har ba itan ba ce.' Ya sake rayawa a ransa, Kodayake Allah ya taimake ta an yi mata irin kwalliyar nan mai canzawa mutum kammani, amma duk da haka ya so ya tantance ta. Da dai ya ga zai shiga ruɗani sai ya yanke a zuciyarsa zai samu wanda zai tambaya don ya tantance. Dalili kenan da ya sanya shi komawa ya zauna har suka gama rawar su suka koma mazauninsu.

Ɗanyar Guba: Cigaban 3--4
Ba ita ta farka ba sai wajajen ƙarfe takwas da rabi na safe, a maimakon ta buɗe ido da addu'a a kan leɓɓanta sai kawai ta buga wata uwar hamma tana miƙa, har sai da ko wace jijiya ta jikinta ta motsa. Can bayan wasu daƙiƙu idonta ya washe sosai ta sauka daga kan gadon ta shiga banɗaki ta wanko fuskarta ta fito, ba zancen sallar asuba a gaban ta, ba kuma wani uzurin ne ya hana ta ba kawai sabo da yi ne wai gawa da gyatsine, don haka sai ta fice zuwa nashi ɗakin.
Ta yi mamakin ganin har lokacin bai farka ba, sai dai hakan bai wani dame ta ba ta je waje tare da buɗe firiza. Kamar yadda ta yi tunani a ciki ya ajiye mata kazar da ragowar lemonta sai kawai ta ɗauko su ta shiga madafa ta kunna gas ta ɗumama kazar ta juye a faranti ta dawo falo. 
Alhamdulillah koda ta tashi ba sauran zazzaɓi ko ciwon kai a tare da ita, hakan ya ba ta damar ta ci ta yi ƙaat kafin daga bisa ni ta je ta ɗora masa ruwan tea ta soya masa wainar ƙwai. Ta juye a faranti mai kyau ta rufe da wani. Kitchen ɗin ta fara gyarawa sai da komai ya koma muhallinsa sannan ta wuce uwar ɗakanta tana karkaɗe shimfiɗa. A lokacin ne ta ji ƙarar buɗe ƙofarsa inda ya fito yana mitsittsika idanu. 
Ɗakin nata ya ƙarasa yana kallon hasken da ke shigowa ta windunan da ta yaye labulen su don ta ga haske sosai, ya fara magana a cikin nannauyar murya "Wai har rana ta fito?"
Ci gaba da cusa fillow a cikin rigar shi ta yi ba ta kalle shi ba ta ce "Da ranar za ta jira har ka tashi ne kafin ta fito?" Bai ce da ita kanzil ba ya juya zuwa inda ya fito ya ɗora alwala ya gabatar da sallar asuba sannan ya sake fitowa ya zauna a kan kujera mai cin mutum ɗaya, lokacin ne ita kuma ta fito cikin adon riga da wando panjamas sai ƙamshi take ta shiga kitchen ta fito masa da abinci ta jere masa a kan ƙaramin table ɗin da ta sanya a gaban kujerar da yake kai.
Sai da ya ƙare mata kallo tsaf kafin ya buɗe ledar biredin a ransa yana faɗar 'Lallai ma matar nan, yanzu cinye kazar ta yi? Da ban ci a waje ba fa?' a zahiri kuma sai ya ce "Ki shirya da wuri na kai ki gidan ƙunshin nan, kin san yau ne fa kamun da Ma'aruf ya gayyace ki, so nake ki yi kyau sosai yadda ba zai ji ciwon ba ki kuɗi masu ciwo ba."
Ta jefe shi da murmushi tana gyara zamanta a kan kujerar da ke fuskantarsa sannan ta ce "Na so na sha'afa ma, amma ba komai za mu iya fita tun ƙarfe goma don daga nan ma ina so zan je saloon, ga zuwa wurin kwalliya ma, yau fa mai wuni ce fitar." Zuƙar shayinsa ya yi ya haɗiye biredin da ke bakinsa kafin ya ce "Ba damuwa Allah dai ya ba mu sa'a." Ta amsa masa da amin sannan ta tashi ta ci gaba da sabgogin gabanta.
***** ******
Da misalin ƙarfe biyar na yammacin ranar ta alhamis Nu'aymah ta yi wa ɗakin taron zobe, a yangance ta ƙarasa cikin hall ɗin lokacin an kashe sautin kiɗa ana ƙoƙarin sauyawa da wani. Ƙarar haɗuwar tsinin takalmin ƙafarta da shimfiɗaɗɗen tiles ɗin da ya mamaye ilahirin hall ɗin ne ya janyo hankalin mafi yawancin mazauna hall ɗin musamman maza. Wasu daga cikin su suka kafe ta da ido ko ƙyaftawa basa yi. A lokacin ne Ma'aruf ya miƙe yana ƙare mata kallo daga nesa. 
Matashiyar budurwa ce da a shekaru ba za ta haura shekara sha takwas ba. Sanye take cikin doguwar rigar yadi light pink mai sassauƙan zane da ya sha adon ƙayataccen ɗinki mai hannun net, rigar ta ɗame jikinta sosai wanda hakan ne ya bayyanar da asirin fasalin jikin nata. Doguwa ce a zubin halitta, siririya a yanayi na ƙirar jiki. Tana da faɗi daga ƙasa cikinta a shafe kamar filasta saman kuma ya yi tudu, a taƙaice dai tana da ƙira irin ta kwalbar fanta, banbancin su da kwalbar kawai shi ne ita bayanta ba a lotse yake ba.
Da murmushi a fuskarsa ya ɗaga duban shi ya sauke idanunsa a kan faffaɗar kewayayyiyar fuskarta mai ɗauke da manyan idanuwa da ɗan madaidaicin hanci da bai yi tsayi can ba kuma bai gajarce ba sai ɗan baki mai ɗauke da Laɓɓa masu kauri da duhu sosai. Fuskar nan ta sha make-up dalilin da ya sanya shi 
tsayawa muhawara da zuciyarsa kenan, yana ƙoƙarin tantance ita ce ko wata.
Kafin ya yi wani kyakkyawan motsi tuni ta ƙaraso gaban shi tana faɗar "My king wannan kallon fa? Ai sai ka sa na tintsire."
Murmushi ya sakar mata da faɗar "Sannu da zuwa Queen mu je mu zauna ko." A dai-dai lokacin ne kuma masu kula da kayan sauti suka sako wata waƙar soyayya ta Ingilishi mai armashin gaske.
Don haka sai waƙar ta saukar musu da yanayi na masoya a fuskokinsu, ba ɓata lokaci suka saƙalo hannun juna suka ci gaba da takowa zuwa mazaunin shi da ke gefen dama na ɓangaren 'yan ango.
Idanu ne suka yi yawa a kansu wasu na yi musu kallon birgewa wasu kuma suna yi musu kallon mamaki. Zahiri ba wai suna mamaki ba ne a kan shigar da ke jikinta saboda ita ce kalar suturar da ke sanye a jikin kowacce macen da ke hall ɗin kasancewar shi ne ankon kamun na mata, kawai dai suna mamaki ne a kan yadda matasan suka saje da yanayi na masoya musamman ga waɗan da suka san Ma'aruf da matarsa sun kuma tantance wannan ba ita ba ce.
Suna ƙarasawa wurin ƙayataccen teburin na musamman da aka tanadar don manyan abokanan ango ya ja mata kujera a kusa da ta Mariya budurwar abokinsa ta zauna a kai shi kuma ya zagaya ɓangaren ta na dama ya ja kujerarsa ya zauna. Da yake table ɗin rounded ne sai aka zagaya masa chairs, babba ne sosai, wurin zaman mutum shida. 
Waiters da suke zagaye a hall ɗin riƙe da teburin abinci na zamani suna turawa ne suka tokare tayar teburin nasu a gaban teburin na su Ma'aruf, sa'annan suka cika musu teburin da kayan maƙulashe da abinci iri-iri. Akan idanunta sauran 'yan matan da ke zaune a kan teburin suka fara cin nasu ba jira, sai dai ita rawanin tsiyar da ta ɗorawa kanta ya hana ta ci duk da yawunta sai tsinkewa suke, musamman da ta sauke dubanta a kan kyakkyawan farantin ƙashin da aka ciki shi dam da snacks dangin su meat pies, donuts, Samosa, cakes, pizza wasu ma har ba ta san sunayen su ba.
"Ki ci wani abu mana Queen." Tana wani shan ƙamshi da ɗage kai ta ce "Ai zan ci ne..." 
Daidai lokacin muryar M.C ta karaɗe ɗakin taron yana faɗar "Yanzu kuma lokaci ne na babban aminin ango wato Ma'aruf Salisu. Idan Ma'aruf yana kusa muna son ganin shi tare da iyalinsa ko budurwarsa a kan wannan dandamali." 
Jin wannan ya sa Ma'aruf ya dubi Nu'aymah da ke zaune a kusa da shi ya ce "Queen mu je ko?" Ba musu kuwa ta miƙe suka jera suna takawa zuwa saman dandamalin.
Mc da yake bakinsa ba mutuwa yake yi ba sai ya hau zazzago zance. "Wow! Abin burgewa, wannan zazzafan aminin angon ya yi katari da zazzafar budurwa, a yanzu kuma lokaci ne da za mu sanya musu kiɗa domin su zazzagar da zallar farincikinsu a wannan ranar, kuma su yi wa amarya da ango kara."
Yana rufe bakinsa ya yi wa D.J umurnin da saka waƙar ƙauna mai armashi.
A hankali suka fara takawa, da ma ga ta gwanar iya rawa sai ta saki jiki sosai suka sha rawa ita da shi, ango Sagir da amaryarsa da sauran masu son su burge Ma'aruf ɗin suka fito suna yi musu ɓarin nera, shi ma Ma'aruf yana yi wa ango liƙin yan ɗari biyar-biyar. 
PSadiq ɗan gidan gwaggwon Salis ya miƙe yana ƙara kafe ta da ido don tun a lokacin da suka zo wuce wa ta gaban shi yake ƙare mata kallo yana son tuna inda ya san fuskar.
'Kai! Kamar matar Salis ce fa.' zuciyarsa ta tsegumta masa, ya so ya yarda da hakan sai ya samu kansa da tuhumar kansa. "Me zai kawo matar Salis a nan, kuma tare da wani saurayi?' ya jefa wa kansa tambayar. 'Amma fa kamar tasu har ta ɓaci idan har ba itan ba ce.' Ya sake rayawa a ransa, Kodayake Allah ya taimake ta an yi mata irin kwalliyar nan mai canzawa mutum kammani, amma duk da haka ya so ya tantance ta. Da dai ya ga zai shiga ruɗani sai ya yanke a zuciyarsa zai samu wanda zai tambaya don ya tantance. Dalili kenan da ya sanya shi komawa ya zauna har suka gama rawar su suka koma mazauninsu.
ƊANYAR GUBA BOOK 1
Na; Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)