YAM CAKE:Hadi Mai Tsinke Yawun Mutum

YAM CAKE:Hadi Mai Tsinke Yawun Mutum

 
 
 
      
 
 
INGREDIENTS(kayan Hadi)
kayan Miya 
Nama
Sugar
Maggi
Doya
Gishiri (Dai-Dai)
Curry
Thyme
 
 
METHOD(Yanda ake hadi)
Dafarko zakisamu doyarki mai kyau guda ɗaya ko fiye da haka. Kifereta kiyanka daidai misali kizuba sugar babban cokali ɗaya aciki saiki ɗaura a wuta.
 
Sannan kiwanke naman kisa thyme kiyanka albasa da maggi guda ɗaya kisa ruwan daidai yadda zaidafa naman harya tsotse saiki kiɗaura akan wuta har yadahu. Idan yadahu saki nikashi kokuma kidakashi da attaruhu kamar biyu tattasai daya kigoga albasa kizuba akan naman bayan kindaka kinsa maggi kijuya yahadu kisoyashi kamar danbun nama amma sama sama kamar minti goma, saiki yanka dafaffen kwai kamar guda uku ko huɗu akai

 
Sannan kikoma kan doyarki data dahu kika sauke harma tafara shan iska, kimurmusheta ko kidaka sama sama kidaidai tadata  sosai saiki zuba maggi da gishiri kisamu prayn pan wanda baya kamu, kizuba mai kamar cokali biyu ko uku
Sannanki raba dakakkiyar doyar zuwa gida huɗu namanma kiraba zuwa gida uku
Saiki ɗauko doyar kashi daya kizuba acikin kaskon kiɗauki naman kashi daya kixuba saman doyar dama kuma kin kada kwanki agefe saiki zuba yalullube doyar danaman saiki sake xuba doyar asaman ƙwan kisake xuba naman daƙwan har kaskon yakusa cika saiki zuba kwan dayawa yadda xai lullubesu gabaɗaya kiɗora awuta ammafa karkibashi wuta sosai kibarshi kamar minti 20/30 kisamu murfin tukunya wanda zairufe kaskon kirufe yadda ƙwan sama zai dahu.
.
Idan yagama saiki samu faranti mekyau ki kwakkwaɓa a hankali zakiga yafita kamar cake saikisa wuka kiyanka yadda kikeso, kuma kina iya gasawa a oven.
Hmmm Aci dadi lafiya!

MRS BASAKKWACE