Daga Awwal Umar Kontagora a Minna.
Madrasatul Nurul Huda Littarbiyatul Aulad, da ke unguwar Barikin-sale da ke cikin garin Minna tayi walimar ɗalibai ashirin da biyu da suka sauke Al-ƙur'ani mai tsalki a yau lahadi.
Tunda farko a bayanin sa, Alhaji Usman Ado Bayero, wakilin sarkin Kano a wajen walimar kuma shugaban gidauniyar Ado Bayero, ya bayyana cewar babu wani mafita ga rayuwar ɗan Adam irin riƙon da littafin Allah, saboda wajibi ne kamar yadda addinin musulunci ya karantar, matakin farko akan haƙƙin ƴaƴa ga iyayensu shi ne karantar da su addini, kulawa da tarbiyarsu, koyar da rubutu, sannan ciyarwa da suturtarwa har zuwa matakin aurar da su.
Bayero, ya cigaba da cewar halin da ƙasar nan ke ciki, wajibi ne iyaye su tashi tsaye wajen sanya idanu akan kulawa da tarbiyar ƴaƴan su, sannan jama'a su tashi tsaye wajen yiwa ƙasa addu'o'in zaman lafiya.
A na shi jawabin, ɗaya daga cikin iyayen da aka yiwa ƴaƴan su wakimar, Garkuwan Talban Minna, Gado Da Masun Bargu, kuma Cika-soron Minna, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida. Ya jawo hankalin iyaye da shugabannin al'umma wajen kula da irin suturar da yara matasa ke sanyawa, musamman ma mata da ke sanya matsattsun suturar da ke bayyana halittarsu, domin fitsara ta watsu a cikin ƙasa, za ka ga yara matasa maza na sanya wanduna wanda bai dace da ƴaƴan musulmi ba, ya zama wajibi a daƙile wanzuwar irin suturar ta baɗala da matasa suka ɗauke shi wayewa, wanda kuma a ƙarahe shi ke zama barazana da kuma yaɗuwar zinace-zinace.
Garkuwan, yace Rabi'atu Sulaiman Babangida ɗaya daga cikin ɗaliban kuma ƴar cikinsa ta baiwa makarantar tallafin dubu hamsin da kyautar Al-ƙur'anai ga ɗalibai ashirin da biyar da ke walimar saukar.
Hon. Isah Abdulƙadir, tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan Neja kuma wakilin Engr. Sani Ndanusa mai takarar kujerar gwamnan Neja a zaɓen 2023, ya yabawa irin gudunmawa da jajircewar malaman wajen karantarwar, yace Engr. Ndanusa yayi alƙawalin bada gudunmawa wajen gida makarantar, ya ƙara jawo hankalin jama'a wajen taimakawa addinin musulunci da dukkanin abinda mutum ya mallaka.
Alhaji Usman Gurara, wani fitaccen ɗan siyasa yayi alƙawalin ginawa makarantar aji a cikin aljihun shi dan samar da ƙarin ajujuwa a makarantar, yace dukkan abinda mutum zai yi a rayuwa bai fi hidimtawa addini muhimmanci ba.
Manyan malaman bangarorin ƙungiyoyin addinin musulunci da ya shafi ƙungiyar IZALA ɓangaren Jos, bisa jagorancin Mu'assas marigayi Sheikh Isma'ila Idris, da Shehunnan ɗariƙar Tijjaniya na daga cikin mahalarta taron.