APC Za Ta Kai Tambuwal, Otom, Da Obaseki Kotu Tana Son A Raba Su Da Kujerunsu

APC Za Ta Kai Tambuwal, Otom, Da Obaseki Kotu Tana Son A Raba Su Da Kujerunsu

 

A wani shiri da ake kallon cewa ka yi na yi maka ne jam'iyar APC ta gama shrin kalubalntar canja shekar da gwamnonin Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Edo Godwin Obaseki da Benue Samuel Otom suka yi zuwa jam'iyar PDP a wa'din mulkinsu na farko. 

Jaridar The Nation ta samu bayanin wannan yunkurin nada alaka da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi na cire gwamnan Ebonyi Dave Umahi kan ya koma APC bayan ya ci zabe a jam'iyar PDP.
Hakan ya sanya APC ta ga dacewar shigar da kara na kalubantar wasu gwamnoni da jagororin PDP da a farko aka zabe su a jam'iyarsu amma suka cika riga da iska suka tafi abinsu.
 
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Otom da Obaseki sun shiga jam'iyar PDP bayan an zabe su a jam'iyar APC a wa'adin mulkinsu na farko.
Majiyar da ta tabbatar da wannan labarin a jam'iyar APC ta ce an hada lauyoyin da za su yi aikin kuma an yi masu bayani kan karar sai dai ba a shigar da maganar gaban kotu ba saboda rikicin shugabanci da jam'iyar ta shiga.
"Gaskiya ne ana cikin shirin kalubalantar wasu gwamnoni da suka bar jam'iya mai mulki zuwa ta adawa, da yanzu magana ta yi nisa ban da aka samu wannan rikicin na shugabanci.
"Tabbas na gaya maka an kammala tattaunawa da lauyoyi da zaran an kare  wannan rigimar ta shugabanci za a shigar da karar," a cewar majiyar.