'Yan Bindiga  Sun Zaftare Kudin Fansan Da Suke Nema Na Mutane 85 a Zamfara 

'Yan Bindiga  Sun Zaftare Kudin Fansan Da Suke Nema Na Mutane 85 a Zamfara 

Ƴan bindigan da suka sace mutum 85 a ƙauyen Wanzamai, cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun amince su karɓi N20,000 a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum ɗaya da suka sace. 

'Yan bindigan sun kuma nemi hukumomi da su janye sojojin da aka kai zuwa cikin ƙauyen a cikin sharuɗɗan da suka gindiya domin sakin mutanen da suka sace, cewar rahoton Punch.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa a ranar Alhamis da ta gabata, ƴan bindigan suka sace kusan kimanin mutum 100 yankin.
Sun bayar da wa'adin ƙarfe 12:00 na daren ranar Lahadi, inda suka yi barazanar halaka duk wani wanda ba a biya masa kuɗin fansarsa ba kafin cikar wa'adin da suka bada. 
Sun kuma yi barazanar cewa idan dai har ba a janye jami'an sojojin da aka jibge a ƙauyen Wanzamai ba, za su cigaba da sace mutanen ƙauyen. 
Wani mazaunin ƙauyen, Abubakar Na'Allah ya gayawa majiyar mu ta wayar tarho cewa ƴan bindiga sun turo saƙo cewa N20,000 kawai za su ƙarba kan kowane mutum ɗaya da suka sace a matsayin kuɗin fansa, duba da cewa talakawa ne marasa ƙarfi. 
“Da farko ƴan bindigan sun nemi da a basu N50m domin sakin mutum 85 ɗin da suka sace waɗanda mafi yawa daga cikinsu mata ne da ƙananan yara da suka shiga daji samo makamashi a ranar Juma'ar da ta wuce. 
“Amma bayan kwashe dogon lokaci ana tattaunawa, sun amince su karɓi N20,000 daga kowane mutum ɗaya da suka sace saboda sun fahimci cewa dukkaninsu talakawa ne." 
Na'Allah ya bayyana cewa iyalan waɗanda aka sacen suna ta ƙoƙarin biyan kuɗin inda ya koka kan cewa da yawa daga cikin su, suna ta siyar da ɗan abinda suka mallaka domin haɗa kuɗin.